Kalaman Soyayya

Wasu Abubuwa Da Suke Hana Maza Magidanta Yin Jima’i

Shahararren marubucin nan a kafar sada zumunta Tonga shine ya kawo wannan bayyani a binciken da sunkayi.

Mata ma’aurata suna yawan kukawa na yadda mazajensu basu cika son yin Jima’i ba. Inda za a ga wani magidanci sai ya dauki kusan mako guda yana tare da matarsa ko matan sa amma bazai yin Jima’i.
Ga wasu abubuwan da suke hana wasu mazan kusantar iyalan su.

Rashin wadatancen bacci na iya hana namiji sha”awar Jima’i.Wasu Abubuwa Da Suke Hana Maza Magidanta Yin Jima'i

Mazan da basa samun wadatuwar bacci a kullum suna cikin kasala. Wannan kasalar ce yake jawo musu rashin son yin Jima’i. Idan kuma sunce zasu yi a hakan, da wuya su iya gamsar da matansu.

Haka nan wasu magungunan da magidanta suke sha suna hana ko kashe sha’awarsu na Jima’i.

Magungunan hawan jini, ciwon suga duk magunguna ne da suke hana maza su kusanci matansu.
Haka nan rashin wadatancen maniyi nan ma yana hana maza kusantar matansu.

Wadata na maniyi yana karawa namiji sha”awar sa, idan testosterone dinsa yayi kasa, dole ne shaawar nasa shima yayi kasa.
Matsala na rayuwa shima yakan hana maza sha’awar Jima’i.
Duk magidancin da yake cikin jarabta na babu, babu sha’awa na Jima’i a tare da shi.
Duk magidancin da bai son matar da yake tare da ita, babu sha’awar kwanciya da ita a tare dashi.

Wadannan kadan ne daga jerin wasu abubuwan dake hana wasu mazan saduwa da matansu. Kamin ki soma kuka da mijinki akan rashin saduwa, yi kokarin gano matsalar.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button