Tsohuwar matar A zango Maryam Ab Yola Ta yi Aure
Majiyarmu ta samu labari daga shafin hausamini inda sunka ruwaito wannan labari.
Inda Lokacin Tana Kan Ganiyarta Ubangidanta A Harkar Ya Aureta, Bayan Aurem Nata Da Yayi Sun Dauki Shekaru Da Aurensu, Sai Daga Baya Kuma Kaddarar Rabuwa Ta Shiga Tsakaninsu.
Bayan Fitarta Daga Gidan Adamu Zango Jarumar Ta Dawo Masana’antar KannyWood, Inda Taci Gaba Da Shirya Fina Finai, Har Sun Taba Yin Wani Film Tare Da Tsohon Mijin Nata Wato Adam A Zangon.
Daga Baya Kuma Jarumar Ta Shiga Harkar Kasuwanci Ka’in Da Na’in, Sai Kuma Tazo Ta Fitar Da Sanarwar Cewa Ta Fice Daga Masana’antar KannyWood Inda Tace Bazata Sake Fitowa A Wani Shiri Ba.. Nan Ne Kuma Ta Koma Ta Rungumi Harkar Kasuwancinta.
Ana Cikin Hakan Ne Kuma Lokaci Guda Sai Allah Ya Nufa Yanzun Ta Sake Wani Sabon Aure, Muna Musu Fatan Allah Ya Tabbatar Musu Da Alkairi Sannan Kuma Ya Basu Zaman Lafiya Mai Daurewa, Amin Summa Amin.
Bidiyon Amarya Maryam Ab Yola Da Angonta