Rigima ta Ɓarke Tsakanin Rahama sadau da Mansurah Isah akan yakin neman zaben Tinubu
Cacar baki ta kaure tsakanin Rahama Sadau da Masurah Isa bisa bayyanar sunan Rahama a cikin jerin sunayen jaruman masana’antun shirya fina-finai na Kannywood ta Arewa da Nollywood na Kudanci da za su kasance cikin ‘yan tawagar yakin neman zaben dan takaran shugaban kasa na APC Bola Ahmed Tinubu.
Jaridar Punch ce ta wallafa sunan Rahama Sadau tare da hotonta daga cikin ‘yan tawagar matan yakin neman zaben tare da wasu manyan jaruman Nollywood Macy Johnson da Joke Sylva a matsayin shugaban kwamitin. Sai dai a sanarwar Rahama kawai aka rubuta.
Ganin wallafar jaridar, Rahama Sadau ta karyata a shafinta na Instagram da cewa ba ita bace tare da nesanta kanta da yanda aka yi har sunanta ya kasance a ciki.
Ita ma Mansura da ta ga abin da Rahama ta wallafa sai ta yi gaggawar bata martani da cewa kuskure aka samu ba sunanta ake tufi ba, sunan Rahama MK ne na cikin shirin Kwana Casa’in.
Martanin na Masurah makar bai wa Rahama dadi ba ganin yadda ita ma ta mayar mata da nata martani da cewa, tana ba wa Mansurah shawarar ta bar maganar nan ta wuce domin bata isa ta ari abin wasu da gadara ta bada hakuri akan kuskuren da aka yi da gangan ba.
Mansura Isa, Samira Ahmad, Tima Makamashi, Fati Nijar, Saratu Daso, Fati Karishma, Kyauta Dillaliya, Hajiya Nas, Momi Gombe da Hadiza Kabara da dai sauran su su ne yan tawagar mata daga masana’antar Kannywood a kamfe din na Tinubu.