Rahama Sadau Ta Lashe kyautar Gwarzuwar Jarumar Ƙasashén Afiríka
Jarumar Fina-finan Kannywood, Rahama Sadau Ta Zama Gwarzuwar Jarumar Fina-finan Ta Kasashen Afirika A (Nollywood) A Gasar Ƙasa Da Ƙasa Ta Toronto, Amurka.
Wannan labarin a duk shine yake ta yawo a kafafen sada zumunta inda shafin labaran kannywood da ke manhajar twitter shine sunka wallafa cewa da fim din Almajiri wanda shine ya baiwa wannan jarumar nasarar lashe wannan kyautar.
“Super Star @Rahma_sadau Tayi Nasarar cinye Gasar Best actress a bikin Toronto International Nollywood Film Festival Canada da film din #Almajiri Muna Alfahari dake #AFRIFF2022″
Super Star @Rahma_sadau ???? Tayi Nasarar cinye Gasar Best actress a bikin Toronto International Nollywood Film Festival Canada da film din #Almajiri ???? Muna Alfahari dake #AFRIFF2022 pic.twitter.com/XzwWO8hAyj
— Labaran Kannywood (@Hausafilmsnews) October 30, 2022
Nan take jarumar ta wallafa sakon jin dadi da murna samun wannan gagarumin nasara da Allah ya bata inda take cewa:-
“Na lashe KYAUTA JARUMAR AFRICA tare da ALMAJIRI a bikin Fina-finan Nollywood na Duniya a Toronto.
Lokacin da na sami sunan, na gaya wa kaina cewa ya isa in yi murna da alfahari. Ban san cewa a zahiri jaririn yana zuwa gida gare ni ba. Abinda ban tsamanin ba.
Godiya ta musamman ga maigidana @aycomian don irin wannan dama mai ban mamaki, da yarda da ni.@tokamcbaror don kasancewarsa sihirin da ya kasance koyaushe. Babu ɗayan waɗannan da zai faru ba tare da ƙirƙirar ku ba. Taya murna ga daukacin tawagar. Yanzu, BA ZAN IYA JIRA DUNIYA TA GA ALMAJIRI BA…
Na gode @tinffestival #MarkYourCalendar #3Dec #Almajiri #BestAfricanActress #Tinff”