Northern Habiscus ‘Malamar Aji’ ta nemi afuwar sheikh Daurawa
Shafin Northern Hibiscus na Aisha Falke wadda aka fi sani da malamar aji ya nemi afuwar Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa kan wallafa hoton a maryarsa.
A saƙon da ta wallafa, Falke ta nemi afuwar malamin inda ta ce, ta wallafa hoton ne don taya shi murna ba don wani abu ba.
Ga abin da ta wallafa a shafinta na facebook
“Malam ai mana aikin Gafara. Mu murna muka taya ka. Amarya masha ALLAH.
Son kowa kin wanda ya rasa. Daga cikin gidan Su Amaryar aka turo mana suma suna murna, ba Su san ran Malan ze bacci ba.
Ai malam hada zuriya da kai abin fariya ne, a cikin murna suka turo.
Amarya malam ya ce kin sha kuka, ki dena kuka lokacin farin ciki ne.
Ayi hakuri
Anyi kuskure.
Munai wa malam fatan Alheri “
Yanzu haka dai tuni Northern Hibiscus ta cire hoton amaryar Malam din da ta wallafa.
Wannan na zuwa awanni kaɗan bayan da Freedom Radio ta zanta da malamin a kan lamarin.
Malam Daurawa ya gargaɗi masu yaɗa hoton amaryarsa da su daina.
A Jumu’ar nan ne Malam Daurawa zai angonce da Gwarzuwar Alƙur’ani ta ƙasa Malama Haulat Amin Ishaq a birnin Gusau na jihar Zamfara.