Matashi ya sheƙa lahira yana tsaka da gwada ƙwazonsa da mace a Otal
Rundunar ‘yan sandan Jihar Ondo ta ce ta fara bincike akan mutumin da ake zargin ya na tsaka da lalata da wata mata a Otal ya rasa ransa a jihar, kamar yadda The Punch ta ruwaito.
An tattaro bayanai akan yada Lanre, mamacin ya zage damtse yana ta lalata da matar a wani otal da ke garin Ondo ranar Laraba da ta gabata.
Har yanzu ba a bayyana suna ko kuma wani bayani dangane da matar ba. Amma wata majiya ta bayyana cewa:
“Matar ta sanar da jama’a ne bayan gane cewa mutumin ya rasu bayan ya kammala wanka daga gama lalatarsu da misalin karfe 9 na daren Laraba”.
“Ihunta ne ya ja hankalin manajan otal din wanda daga bisani ya gayyaci ‘yan sanda daga ofishinsu da ke Enu-Owa don bincike.”
Kakakin rundunar ‘yan sandan, Mrs Funmilayo Odunlami ta ce mutuwar tasa ba ta lafiya lau bace, yayin da aka tuntubeta don jin bayani.
Amma a cewarta, yanzu haka ‘yan sanda sun shiga lamarin dumu-dumu don gano asalin silar mutuwarsa. An tattaro bayanai akan yadda aka dauki gawar mamacin, inda aka kai ta ma’adanar gawa da ke jami’ar Kimiyya da ke Ondo.