Mata ta kashe mijinta da guba a Borno
Rundunar ‘yan sandan jihar Borno ta ce ta kama wata matar aure, mai suna Fatima Abubakar ƴar shekara 25 bisa zargin kashe mijinta, Goni Abbah da guba.jaridar Daily Nigerian na ruwaito
Kwamishinan ƴan sanda a jihar, Abdu Umar, wanda ya bayyana haka ga Kamfanin Dillancin Labarai na Ƙasa, NAN, a Maiduguri, ya ce jami’an ƴan sanda sun kama wacce a ke zargin ne a ranar 19 ga watan Oktoba a Anguwan Doki.
Malam Umar ya ce wanda abin ya shafa, wanda shi ne babban Limamin unguwar, ya dawo daga masallaci ne a lokacin da wacce ake zargin, wadda ita ce matarsa ta biyu, ta zuba guba a cikin abincinsa.
Ya bayyana cewa Goni bai daɗe da fara cin abincin ba sai gubsr ta fara yi masa aiki, inda nan da nan ya shiga wani hali.
A cewarsa, nan take aka garzaya da mamacin zuwa asibitin kwararru na jihar, inda aka ba shi kulawar gaggawa, amma abin takaici daga baya ya rasu bayan sun dawo gida.
Nan take kwamishinan ƴan sandan ya baza jami’an hukumar binciken manyan laifuka da leken asiri domin cafke wacce a ke zargin bayan da iyalan mamacin suka kai rahoton faruwar lamarin a ofishin ƴan sanda na GRA.
Ya ci gaba da cewa, da zuwan ƴan sandan, sai su ka ga dandazon matasan unguwar da su ka fusata kuma ke ƙoƙarin afkawa gidan wacce s ke zargin da nufin halaka ta, amma ‘sai yan sandan su ka samu nasarar shawo kan lamarin.
Ya kara da cewa, wacce ake zargin a cikin bayananta ta, ta amsa laifin da ake zargin ta da shi, inda ta ce ta sayi gubar ne a kasuwar Monday Market a lokacin da ta riga ta yanke shawarar kashe shi.
Ya ce an rubuta bayanan a matsayin laifin kisan kai a ofishin daraktan kararrakin jama’a kafin a gurfanar da ita a kotu.
Wacce ake zargin mai suna Fatima da aka kama, a ofishin ‘yan sanda, ta shaida wa NAN cewa ta kashe mijinta ne saboda ta gaji da auren.
Ta ce: “Ban taɓa son auren ba. Goni shine mijina na biyu; Na rabu da mijina na farko saboda na tsani aure.
“Duk lokacin da na farka na tuna cewa ni matar aure ce, abin ya na ba ni haushi. A wani lokaci ma sai da na gudun wurin iyayena don neman a kashe auren nawa, amma kullum sai su mayar da ni, suna neman na yi hakuri,” in ji ta.