Kalaman Soyayya

Kalaman Soyayya Masu Kara Dankon soyayya Ga Masoya

Idan kana tare da budurwa masoyiyarka, ya kasance kanayi mata kalamai masu dadi na jan hankali, wadanda zasu dinga faranta mata rai.

KAMAR HAKA! Na dade ina kallon taurarin samaniya yayinda naga wacce tafi kowacce haske, saina naga bakowa bace nike ganiba sai ke masoyiyata! So gamon jinine, haqiqa sonki ya zamo jinin jikina! Kinfita daban a cikin mata, duk lokacin da na kallleki, sai naga kamar babu kyakykyawar wace sai ke! Ki kwantar da hankalinki masoyiyata babu wata a zuciyata sai ke kadai! Yarda da amincewarki gareni, sune zasu tabbatar da soyayyarki tagaskiya a gareni!Kalaman Soyayya Masu Kara Dankon soyayya Ga Masoya

Farin ciki baya dorewa a rayuwa sai tare da bakin ciki, dan haka kowane hali nike bazan ta6a mantawa dake ba masoyiyata! Nakan raba dare ina mai roqon Allah don neman biyan buqata, ko kinsan kece abu na farko da nike roqo samu! Yanayin sanyi kan sa mutum ya takura, tare da lullu6a da qaton mayafi amma ni duk sanyin da ake idan na tunaki sai naji tamkar yanayin zafi! Kamar yadda kowacce bishiya kanyi rassa a sama, kuma tayi saiwa a qasa, haka sonki ya mamaye dukkan jikina, idan na kalleki sai nayi farin ciki, idan naji tattausan muryarki, sai nishadi da walwala tare da annashuwa gami da farin ciki su mamaye zuciyata!

Abokina ahakan zaka bi don sace zuciyar masoyiyarka cikin sauki!! Kema zaki iya juya turn na wannan kalaman domin sace zuciyar masoyinki cikin sauki!! In kuma kinyi musu ku jaraba kugani!!.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button