Kalaman Soyayya masu dadi : Yadda Zaki Fahimci Saurayinki Yana Matukar Sonki
Akwai wasu alamun da mace zata iya fahimtar masoyinta na matukar sonta. Da kuma wadannan alamun ne zata iya yanke hukunci akan mai son nata da yake nuna mata irin wadannan alamun ko wanda bai nuna mata.
Ga wasu alamun da mace zata iya fahimtar namijin da yake soyayya da ita yana matukar sonta.
1:Idan namiji na sonki da gaskiya ba zai taba miki karya ba. Duk wani abunda zai fadamiki babu zancen romon baka zance ne na gaskiya tsakaninsa da Allah.
Mai sonki da gaskiya duk wani abunda zai fadamiki yana gudun fadamiki abunda bai tabbatar ba.
Da zaran kin fahimci namiji yana da wannan alamun tabbas da gaske yana sonki.
2: Mai sonki da gaskiya yakan zabi kalaman da zai furta miki.
Idan namiji na sonki ba zai taba yarda ya furta miki kalaman da zasu cutar dake a lokacin farin ciki ko bacin rai.
3: Idan namiji na sonki tsakani da Allah bai gajiya da kasancewa dake.
A kullum da son samu ne ya kasance kusa dake. Bai da juriyar yin nesa dake. Wannan alamu ne na soyayya na gaskiya.
4: Wanda yake sonki yakan shiga matukar damuwa a lokacinda kike cikin damuwa. Yakan fiki farin ciki a lokacinda kike cikin farin ciki.
Namijin da yake miki soyayyar gaskiya bai da sukuni har sai ya tabbatar da cewa ya fitar dake daga duk wata matsalar da kika shiga.
5: Idan namiji na sonki bai gajiya da miki gyara a duk lokacin da kika yi kuskure. Mai sonki na gaskiya bai gajiya da nuna miki abunda yafi dacewa da rayuwarki.
A kullum burinsa ya karfafa miki gwai tare da tallafa miki domin ganin kin cimma burinki da kika saka a gaba.
Wadannan wasu ne daga cikin alamomin da mace zata fahimci namijin yana matukar sonta.
Ba su bane kadai alamun ba. A darasin mu na gaba zamu ci gaba da kawo wasu daga cikin hanyoyin da mace zata fahimci namiji na sonta.