Kalaman Soyayya Masu dadi: Ga Wasu Ginshikai Da Zaka Gina Soyayyar Ka Akansu
Soyayya tamkar gine, idan kayi da kayan ginin da basu da inganci gaba kadan kinin na iya ruftawa ko ya lalace tun kamin ma a gama ginin.
Don haka idan zaka gina soyayya ka tabbatar da cewa ka ginashi da kayan gini masu inganci domin dorrwarsa.
Ga wasu ginshikan da zaka iya daura soyayyar akansu.
1: Gaskiya- Kada ka sake ka soma yin soyayya da karya ko yaudara.
Shi soyayya na aure ba kamar soyayya na shashanci bane, namiji baya zuwa da karya ko yaudara.
Asalna idan kai mai akwai ne ko mai matsayi kada ka nuna mata hakan har sai idan itace ta fahimci hakan.
Muddin zaka gina soyayyar ka cikin gaskiya da babu yaudara. Tabbas cikin saukin zaka mamaye zuciyarta har abada.
2: Yarda Da Amana- Muddin zaka saka hakan cikin soyayyar da kake yiwa mace, tabbas zaka samun soyayya mai gargo daga gareta.
A duk lokacin da ka fahimci zuciyarka ya kasa kwanciya da macen da kake nema da aure, to idan da hali ka hakura kawai domin nan gaba auren zai rushe.
Soyayyar aure tun a farko ake baiwa juna aminci da yarda yadda duk wanda ya nemi zaluntar guda, Allah na iya tona asirin hakan.
3: Ka Kiyaye Kalamanka: Duk wasu kalamanka cikin farin ciki ko bacin rai ka kiyayesu wajen furtawa macen da kake so su.
Mata suna da rikon abunda yayi musu zafi da abunda yayi musu dadai. Har abada basa manta wadannan kalaman daga wajen wanda ya furta masu su.
Don haka ka kyautata kalamanka ka kuma furta mata abunda zai yiwu ba abunda kawai dadi ko farin ciki yasa ka fadesu ba.
Muddin kana da wadannan abubuwan zaka gina soyayyar ka cikin aminci da kauna.
5: Ka So Wacce Take Sonka, kada ka taba neman dole sai ka turawa mace sonka da kaunarka karfi da yaji. Kayi kokarin samun soyayyar mace ta hanyoyin sace zuciyarta amma ba bin hanyoyin da za a shawo maka kanta da dole ba.
Ita mace idan tace bata so tun a farkon aka takurata ta dawo tace tana so. Ka bata lokaci sai wannan batason ya sake dawowa koda kuwa bazata rabu da mutumin ba amma har ta gama rayuwa dashi a batason nasa take.
Don haka ka so wacce take sonka ka rabu da duk wata macen da zata baka wahala musamman wance tun a farko ta nuna maka batada ra’ayinka.