Iyaye Mata: Yadda Zaki tashi Jaririnki Daga Bacci da yanayin yana jin yunwa ko ya koshi
Ta yadda zaki iya masa wanka da bashi nono
JARIRIN DAKE CIKIN Bacci…
Yayin da zaki tashi jaririnki daga barci musamman don yin wanka kada ki jijjiga shi, kada kuma ki ɗauko shi ki danna a ruwan zafi kamar yadda ake yi sai dai inyaji ɗumi ya buɗe ido. Abinda za kiyi kawai ki rika hura iskar bakinki a tsakiyar kan shi, wannan itace kyakkyawar hanyar farkar dasu.
BAYAN JARIRI YA FARKO BARCI
Idan yaronki ya farko daga barci musamman cikin kuka, wasu kokarin bashi ruwa suke fara yi kafin daga bisani a saka shi a nono. Wannan kuskure ne. Nono zaki fara ɗora mishi ya sha sa’dda ya farko daga barci. Ba shi ruwa irin wannan lokacin kan jawo musu zawo da ƙanƙancewa.
YA ZAN GANE YANA JIN YUNWA ?
Idan kika ga jaririnki yana yawan ƙwalla wato hawaye na yawan kwaranyowa daga idanu shi ba tare da yin kuka ba; Toh alama ce ta nono baya isar jaririnki wannan shine alamar dake miki nuni domin ba baki gareshi ba.
Don haka, musamman mata masu haihuwar fari basu cika fahimtar hakan ba, wani lokacin harma da waɗanda suka daɗe suna haihuwar don haka a saka a ido a kula , a tabbatar ana samun ingantacciyar shayarwa.
*TA YA ZAN GANE JARIRINA YA ƘOSHI?*
Daga lokacin da kika ga jaririnki yana cillo fitsari abin shi, nan da nan sai aji ya malalo fitsari, to wannan alama ce ta nono na isar shi, ma’ana yawan fitsarin jariri shike nuni da ingantacciyar shayarwa.
*ME ZAI TAIMAKA MIN IN GANE YARON YA ƘOSHI?*
Eh wasu kanyi kuskure idan nono ya suɓuce daga bakin Yaro sai su dauka kawai ya koshi ne, ko kuma ta ƙosa tayi wani abu don haka ko ɗan yaya ya Jima sai kaga uwa ta janye nono ta tashi in dai ba kuka taji ya saka ba,
Don haka duk macen dake haihuwa ta Sani, Yaro Kan Jima ne yana tsotso ƙarshenta dalili na baki haɗa shi da jikinki ya kama nonon sosai ba, don haka kaɗan yake zuwa shi yasa yake daɗewa kuma kike Jin zafi domin Kan kawai kike ɗosana masa, uwa- uba irin wannan shiriritar shayarwar ke saka cikin Yaro kumbura saboda iskar da yake zuƙa haɗe da nono, wannan ke sa wani jaririn ya yita kuka, ko a ga yayi kwanaki ba kashi.
Don haka, ki zauna guri ɗaya ki nutsu, ki kuma dunga goge Kan nononki duk sa’anda ya gama sha da ruwa, kada kawai ki jawo bra ki saki anjima kuma ki ƙara ɗaga mishi ki cusa bakin shi, hakan zai sa ya ji ƙarnin da zai hana shi kamawa ko kuma ƙwayoyin cutar da ke jikin fatarki ta nishi gurin yaronki ya tsotsa ya kama gudawa duk ya lalace ƙanƙanin lokaci.
Don samun kyakkyawar shayarwa ki kiyaye: ban da ba da nono a kwance komi gajiya, komi dare ki tashi zauna ki sanya shi a cinya haka zai hanashi kumburin ciki, sannan idan yasha kika ga alamun kamar ya isa ya ƙoshi to ki ɗauke shi ki saka shi a kafaɗarki, ki riƙa shafa bayansa zuwa can za ki ji yayi gyatsa, wannan alama ce ta ya ƙoshi kuma nono ya tsirga masa ciki kya iya mayar da shi ki kwantar.
In ko ba ki ji yayi gyatsa ba to fa duk daɗewar da kika yi ki sani nono bai ishe shi ba don haka ki mayar da shi ya ƙara.
Wannan bayanin ba ga mata ba kaɗai, kaima a matsayin ka na Maigida Kana da rawar da za ka taka don ganin kun kula da jaririnku. Sannan a tabbatar ana samarwa da mahaifiyar isashshen abinci mai inganci domin lafiyarta itace lafiyar jaririn.
Dafatan bayanin ya ilmantar.
Idan ya ilmantar to ka/ki yi Mana sharing zuwa gaba.
Allah yabamu xuriya dayiba