Inajin Takaici da bakin ciki yadda mutane ke aibanta yan fim – Yasmin Kwana casa’in
A yau din nan majiyarmu ta hausaloaded ta samu wani labari da gidan rediyo Freedom kano inda sunka zanta da wata matashiyar yar fim wnada tayi fice a cikin shiri mai dogon zango da gidan talabijin na arewa24tv ke gabatar kwana casa’in.
Jarumar Fatima ta bayyani irin rashin jindadin ta na yadda mutane ke nunawa jaruma kalmomi wadanda basu dace ba ga yadda zantawar ta kaya.
“Jaruma Fatima Isah Bala wadda aka fi sani da Yasmin a shirin Kwana Casa’in ta nuna damuwa kan yadda wasu mutane ke aibata ƴan film.
Yasmin ta bayyana hakan ne a zantawarta da Freedom Radio.
Ta ce, har a zuciyarta bata jin daɗin yadda mutane suke aibata ƴan film har ta kai ga ƙin aurensu.
Jarumar ta ƙara da cewa a halin yanzu bata da burin da ya wuce ta yi aure.
Fatima Isah Bala wadda mawaƙiyar gambara ce kuma jaruma, wadda ta fito a ƴar gidan AVM Adnan a shirin Kwana Casa’in na Arewa24″