Labarai

Farfesa ya shawarci matasa da su riƙa hada-hadar kuɗin yanar-gizo

Wani tsohon Malamin Jami’ar Bayero da ke Kano, Farfesa Aliyu Abdullahi Jibiya, ya yi kira ga matasa da su ci gajiyar kasuwanci da kudaden intanet da suka mamaye duniya a wannan lokacin. Shafin Daily Nigerian Hausa

Farfesa Jibiya ya bayyana cewar kuɗin kasuwanci na yanar gizo mai suna ZUGACOIN ɗaya ne daga cikin wadan da suka fi shahara a harkar kudin yanar gizo a duniya.

Aliyu Jibia, ya bayyana haka ne a yayin da wata Jaridar mai suna Daily Post ta yi bikin karrama shugaban gidauniyar SAMZUGA, wanda ya shahara wajen hadahadar kasuwanci da kwandalolin intanet.Farfesa ya shawarci matasa da su riƙa hada-hadar kuɗin yanar-gizo

Jibiya ya bayyana cewa, “Archbishop Farfesa SamZuga wanda yake zaman jami’in diflomasiyya a tsarin ‘INTERNATIONAL SOCIETY OF DIPLOMATS AND GLOBAL EMISSARY COUNCIL’, wanda shine shugaban kula da sashin tattalin arziki na farko a tsarin IT na duniya.”

“Samzuga na cikin farko+farko a fannin tattalin arziki a tsarin kudin yanar gizo na duniya, kuma shi ne farkon wanda ya kafa cibiyar hada-hadar kasuwanci a Afirka.”

Farfesa Jibia, ya kuma kara da cewa, ” Samzuga wanda ya samar da kwandalar ZUGACOIN, na daya daga cikin kamfanoni 3 da suka fi shahara a harkar kudin yanar gizo a tsakanin ‘yan Najeriya dake warwatse a duniya.”

“Archibishop Farfesa Sam Zuga, limamin coci ne a Najeriya da ke zaune a Dubai, dan kasuwa ne mai taimakon jama’a, ya samu lambar yabo ta digirorin girmamawa daga jami’o’i daban-daban a duniya, ciki har da wasu jami’o’in kasar Amurka.”

“Haka kuma, Archbishop Farfesa SamZuga, mamba ne a kungiyar ‘yan kasuwa ta Dubai, kuma dan Najeriya na biyu da ya karbi lambar yabo daban daban a fannin zaman lafiya a kokarinsa na samar da zaman lafiya da fahimtar juna tsakanin al’umma a ciki da wajen Najeriya, haka kuma, an taba bashi lambar yabo ta Jakadan Majalisar Dinkin Duniya kan zaman lafiya.

“Archbishop Farfesa SamZuga, yana da lasisi a Dubai wanda ke ba shi damar shigo da zinari daga sassan duniya zuwa Dubai, kuma shi ne ya samar cibiyar kasuwanci ta yanar gizo don kawo shirye – shiryen sauyin yanayi wanda aka sanar a hukumance a taron sauyin yanayi na Majalisar Dinkin Duniya, wannan manufar ita ce kawar da radadin matsin lamba na rayuwa ga masu karamin karfi.”

Da yake jawabi a wajen bayar da kyautar, Editan Hausa Daily Post, Abdulrazak Ahmad Jibia, ya ce an karrama Archbishop Farfesa Sam Zuga ne dangane da sadaukar da rayuwarsa da ya yi wajen gina rayuwar al’ummar Afirka a karkashin gidauniyar SAMZUGA, musamman batun kiwon lafiya kyauta, koyar da mutane sana’o’in hannu da dai sauransu.

A jawabinsa yayin karbar lambar yabo, Farfesa Mkpa Ogoh Mkpa, wanda ya wakilci Archbishop Farfesa Sam Zuga, ya gode wa Allah Madaukakin Sarki da gaisuwa ta musamman ga jaridar Hausa Daily Post, bisa karramawar da aka yi masa, ya kuma tabbatar da cewa Archbishop Farfesa Sam zai ci gaba da yin iya kokarinsa, zai kara himma wajen samar da sabbin abubuwa don ciyar da al’umma gaba kamar yadda ya saba.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button