Dole mawaƙi Rarara ya kai waƙoƙinsa Hukumar Tace Finafinai don a tan-tance su – Gwamnatin Kano
A dai dai lokacin da dan gantaka ke ƙara ƙamari tsakanin fitaccen mawaƙin siyasar nan Dauda Kahutu Rarara, da jami’an gwamnatin jihar Kano, bisa zargin gwamnan jihar Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje da yin uwa da makarɓiya wajen cire sunan mawaƙin daga cikin jerin sunayen ‘yan kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na tutar jam’iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu. Shafin labarai24 na ruwaito.
Tun da aka tsayar da Mataimakin Gwamna, Nasiru Yusuf Gawuna, ba a ji Rarara ya yi masa waƙa ba.
An dai jiyo mawaƙin ya yi wa ɗan takarar gwamna a jam’iyyar ADC, Sha’aban Sharaɗa waƙa.
To sai dai ana tsaka da wannan dan barwa ne a ka jiyo ɗaya daga cikin hadiman gwamnan kuma mai baiwa gwamnan shawa kan sha’anin Farfaganda wato fitaccen jarumin barkwanci Mustapha Badamasi wanda akafi sani da Naburaska, na jaddada cewa dolene mawaƙin ya fara kai waƙoƙinsa Hukumar Tace Finafinai Da Ɗab’i Ta Jihar Kano, domin a fara tan-tance waƙoƙin sa.
Labarai24 ta rawaito cewa ta cikin wani bidiyo da jarumin ya wallafa a kafar sada zumunta ta zamani ya ce” ina so Rarara ka dakata haka, Abdul Amart nawa ne shi ma Rarara nawa ne to, sai dai ta wani ɓangaren ka saki layi”.
” don haka duk waƙar da kayi ka kaita Hukumar Tace Finafinai ta tace, in kaƙi ka kai to kuwa zaka jawowa shi shugaban Tace Finafinan domin aikin sa ne”. A cewar Naburaska.
Duk da dai maganganun jarumin na zuwane ta sigar shaguɓe ga Shugaban Hukumar Tace Finafinai duba da yadda a baya aka samu rashin jituwa tsakanin jarumin da Hukumar kan yadda hukumar ta shahara wajen kama wasu daga cin mawaƙan da basa cikin tsarin tafiyar gwamnatin APC, kafin ayyana ficewarsa daga tsagin tafiyar ɗan takarar shugaban ƙasa a ƙarƙashin jam’iyyar NNPP Dr. Rabi’u Musa Kwankwaso zuwa gwamnati mai ci ta APC.
To sai dai har zuwa yanzu mawaƙin bai magantu ba kan wannan batu.