Buhari ne ya amince da sake fasalin Naira, CBN ya mayar wa da ministar kudi Martani
Babban bankin ya kuma ce ya bi tsarin da ya dace wajen sake fasalin takardar Nairar.
Kakakin Babban Bankin na CBN, Osita Nwanisobi ne ya bayyana haka a lokacin da ya ke mayar da martani ga Ministar Kudi, Kasafi da Tsare-tsare ta Kasa, Zainab Ahmed, inda ta ce ba a tuntuɓi ma’aikatarta lokacin da ake shirin kaddamar da tsarin ba.
A lokacin da ta bayyana a gaban kwamitin majalisar dattawa a jiya Juma’a, ministar ta yi watsi da shirin, wanda ta bayyana a matsayin bai dace da halin da ake ciki yanzu ba.
Sai dai Nwanisobi ya bayyana mamakinsa da ikirarin na ministar, yana mai jaddada cewa CBN ya kasance cibiya ce mai bin ka’idoji.
Ya ce hukumar gudanarwar CBN ta yi amfani da tanadin sashe na 2(b) da sashe na 18(a) da sashe na 19 (a) (b) na dokar CBN ta shekarar 2007.
Da yake kira ga ƴan Nijeriya da su marawa aikin sake fasalin kudin kasar baya, kakakin ya ce hakan yana da amfani ga ƴan ƙasa baki daya, yana mai kara jaddada cewa wasu mutane na tara makudan kudade a wajen rumbun bankunan kasuwanci.
Wannan al’amari, a cewarsa, bai kamata duk wanda ke nufin alheri ga kasa ya karfafa shi ba.