Labarai
Ba zan yi hirar kuɗi da wanda bai samu dala miliyan 100 a bana ba — Burna Boy
Ya bayyana hakan ne ta InstaStory a shafinsa na Instagram a jiya Lahadi, inda ya ce, “Ba zan iya yin magana ta kuɗi ba idan ba ku samu $100m a wannan shekara ba.”
Hakan na zuwa ne sa’o’i bayan abokin aikinsa, Wizkid ya yi alfahari game da adadin dukiyar da ya tara.
Wizkid har ma ya yi alkawarin buɗe aji ga masu sha’awar su zo su koyi yadda za su sami duk abin da su ke so da kuma iya tattala kuɗi.