Ba Duk Mata Masu Saka Sarka A Kafa Suke Maɗugo Ba
Akwai mummunan zato da mutane da dama suke yiwa mata masu saka sarka a kafafuwansu.
Wasu na yiwa irin wadannan matan kallon karuwai, masu suna musu kallon’ yan kungiyan asiri wasu kuwa suna masu kallon mata ne da suke neman mata yan uwansu da lalata.
Shi wannan tunanin ko zargin akwai kuskure matuka kuma mai girma a tare dashi. Wannan kuskuren ya raba masoya da ma’aurata da damar gaske.
Ba wai masu saka Sakar a kafuwansu kadai wannan zargin ya shafa ba. Har ma da matan da suke saka zobe a kafafuwansu suma ana musu irin wannan kallon.
Sama da shekaru 8000 da suka wuce tarihi ya nuna mata suna amfani da sarka a kafa a matsayin abun ado da kwalliya. Wannan kwalliyar kuma ya samo asali ne daga matan Kasar Masar. Sune tarihi ya nuna suka soma amfani da shi wajen yin kwalliya ga mazaje su da kuma yiwa sarakunan su da masu kudinsu rawa. Wanda wannan abun ya yadu zuwa sauran kasashen duniya har ƙabilun Hindu suka karbi kwalliyar tamkar sune suka kirkiro shi saboda yadda ya dace da al’adarsu.
A shekara na 1930 zuwa karni da 20c a wannan lokacin ne wannan kwalliyar ya samu karbuwa wajen turawa da Amurkawa. Wanda har wannan lokacin da muke ciki matan suna kwalliya da shi a kafafuwansu.
Ba saboda kwalliya ko rawa ba kadai. Saka sakar a kafa a wancan lokacin yana nuna isa da mulki da kuma kudi. Domin wasu matan suna saka sarka zinari ne ko azurfa domin nuna isa. Kuma tabbas ko a addinace Malamai sun tabbatar da halaccin mata suyi kwalliya da sakar a kafafuwansu muddin ba zai rika ƙarar da zai jawo Hankalin maza ba a lokacin da suke tafiya. Wannan shine asalin saka Sakar a kafafuwan mata.
Kamar yadda ayar Alkurani yazo da shi a Aya na 31 na suratul An-Nur. Wanda su matan Larabawan jahiliya idan suna tafiya da sarkar a kafafuwansu hakan yana yawan yin sautin dake dauke hankali mutum yadda dole sai ya juyo ya ga wacce ke wucewa. Amma Allah bai haramta musu ba sai ya hanasu buga kafafuwansu yadda sarkar sai yi sauti. Wanda shi na yanzu da matan ke sakawa bai da wannan sautin.
Sai dai kuma da zamani ya shigo sai aka samu wasu matan da suke juya wannan manufar na saka sarka a kafafuwansu a maimakon na kwalliya sai ya dawo suna amfani da shi a matsayi wani alami ne na kungiya.
Tabbas mata ‘yan maɗugo da mata masu Sana’ar karuwanci suna amfani da sarkar kafa a matsayin alaminsu. Amma hakan kuma rashin adalci ne mutum yace ko ya dauka duk macen daya ganta da sarƙa a kafa tana wannan harkar.Kuskure ne babban wani ya yiwa abun tunanin hakan. Kawai masu kin wannan kwalliyar wadanda suke da tsananin kishi ne da kuma rashin fahimta baya ga jumudanci da sunan addini da basu ma fahimci addinin ba.
Irin mu da mukayi yawon duniya dai da gwargwado naga kasashen da hatta tsuhuwa ‘yar shekaru 80 da yarinya’ mai shekaru 5 kacal suna sakawa.
Haka nan babu bambamcin al’ada ko addini wajen kwalliya da sarka kafa domin kowace mace tana sawa.
Babu wani jami’in tsaro da yake da wata hujjar bibiyan mutum saboda yana da wani alami na kwalliya. Koda kuma suna hakan suma suna yi ne akan zato. Ko masu yin Tattoo ba dukkanninsu bane yan kungiyan asiri ba. Tattoo shi ma yana da nasa asali.
Nayi mu’amla da mata masu harkar madugo da dama ciki harda shugansu na yankin arewacin kasannan amma ban taba ganin sun da sarka a kafa ba.
Mace ba sai ta saka sarka bane take zama ‘yar madugo ba. Shi wannan harkar cult ne, idan mace tana yi koda sau daya tayi da fitattun cinsu to sun san da zamanta ba sai ta saka sarka a kafafuwanta.
Don haka masu zargin mata haka nan kawai ba tare da wani hujja ba, kada su manta Allah Ya yi maganar hukuncin da zai musu littafinSa.
Sai dai kawai yana da kyau matan su kiyaye su kaucewa abun da za a zarge su da shi koma menene shi.
Yadda ba duk’ yan ta’adda da suke kashe mutane da suna musunci ba musulmai suke wakilta ba, haka matan da suke saka sarka a kafafuwansu ba ‘yan madugo suke wakilta ba.
Ana iya samun ‘yar maɗugo ko Karuwa da take saka wannan sarƙa kawai da sunan kwalliya bata ma san cewa ana mata kallon hakan ba kuma ita din kuma hakance. Akwai wata da ba maɗugo take ba kuma bata ma san cewa yan maɗugo suna amfani da shi ba a matsayin alaminsu kawai ita kwalliya take yi dashi.
Wasu matan kuma suna kwalliya da shine ganin wata gwanarta na shirin fim ko mawakiya tana sakawa shi ya bata sha’awar sakawa.
Babu shakka akwai wasu ɗabi’u ko halaye da suka siffantu da wasu mutane can ɓata gari. Wanda asalin su daman su bata garin ne suka kirkosu. Wannan dole mutum ya kaucewa alamta kansa da shi.
Akwai kuma wasu ɗabi’u da halaye wadanda asalin su masu kyau ne amma wasu ɓata gari suka gurbata shi, kamar saka Sakar a kafa. Irin wannan saurin yanke wa mutum hukunci na zato mara kyau kuskure ne babba kuma zunubi ne don haka a kiyaye.
Idan baka ra’ayi matarka ko wacce ka isa da ita ta saka, kada ka haramtawa irina da banda sarka so nake naga an saka mini jigida, an huda mini hanci, baki dama cibiya yadda zanji dadin wasa dasu.