An yanke wa dan fim ɗin Amurka, Kaalan Walker hukuncin shekara 50 a gidan yari bisa laifin fyade
Kalan Walker, dan wasan kwaikwayo na Amurka kuma mawaki, ya samu hukuncin daurin shekaru 50 a gidan yari bayan samunsa da laifin yiwa wasu mata bakwai fyade; mata hudu da ƴan mata matasa uku
Daily Nigerian Hausa na ruwaito Ƴan sanda sun ce, “Wadanda abin ya shafa, wadanda masu sana’ar tallan kaya, sun yi zargin cewa Walker ya kai neme su ta kafafen sada zumunta na yanar gizo don ya taimaka musu a harkar sana’ar su,” amma lokacin da wadanda abin ya shafa ke kadaita da shi, sai ya yi lalata da su.
Kaalan, wanda aka yanke wa hukuncin a ranar Litinin, zai jawo wadanda abin ya shafa zuwa wurare ta hanyar gaya musu cewa akwai wani hoton bidiyo na waka ko kuma zai gabatar da su ga wani sanannen, in ji City News.
Benzema ya lashe kyautar Ballon d’Or karo na farko a rayuwarsa ta ƙwallon ƙafa
Karim Benzema ya lashe kyautar zakaran ƙwallon kafa na shekara mai suna Ballon d’Or a karo na farko a rayuwarsa ta ƙwallon ƙafa.
Kyautar dai ta zamto lada ne ga gagarumin ƙwazon da Benzema ya yi a kakar wasa ta 2021-2022.
An dai bada kyautar ne a wani biki da ya gudana a wani dakin taro na Theatre du Chatelet da ke Paris.
Kyaftin din Real Madrid Benzema, ya kasance wanda aka fi sa ran zai lashe kyautar a jiya Litinin bayan da ya ja ragamar da kungiyar ta Spain zuwa nasarar lashe gasar cin kofin La Liga da na Champions League a bara.
Gabanin gasar cin kofin duniya ta FIFA a watan Nuwamba zuwa Disamba, an canja tsarin cancantar lashe kyautar Ballon d’Or bisa ga kwazo a wasanni na yau da kullun a kaka a karon farko.
A maimakon a da sai a kan ƙwazon da ɗan wasa ya yi idan an shiga wata kakar wasannin.
Sai dai kuma dan wasan Faransa Benzema ya kasance kan gaba a kowane hali.
Sai gashi shi ne ya lashe gasar bayan ya zura kwallaye 44 a wasanni 46 kuma ya samu kambu na biyar a Turai a kakar 2021-2022.