Alfanun Jima’i Kafi Shayi Ga Ma’aurata
Kafi shayi, shine sunan da masu iya magana suka sanyawa Jima’i da ma’aurata suke yinsa da safiya.
Daga lokacinda alfijir ya keto har kamin fitowar hantsi,duk wannan lokaci ne na yin Jima’in Kafi Shayi.
Ma’aurata da dama suna yin wannan Jima’in ne ba tare da sunsan cewa yana da matukar amfani ga rayuwarsu na aure ba.
Ga wasu alfanun da Jima’in Kafi Shayi yake samarwa ma’aurata kaman yadda masana sukayi bayani.
1: Motsa Jiki: Shi wannan Jima’in na matsayin yin motsa jiki ne ga ma’aurata. Don haka duk ma’aurata da suke yin kafi shafi ba sai sunyi wani motsa jiki Na daban ba wannan ya wadatar.
Irin kasalan nan da mutum yake tashi dashi daga bacci, idan ma’aurata sukayi kafi shayi da kuzarinsu zasu taso.
2: Warware Gajiya: Ko da mutum yayi wawan kwanciyar da ya saka jikinsa ciwo. Muddin zai samu Kafi Shayi nan take jikin nasa zai warware.
Ma’auratan da suke yin kafi shayi basa tashi da ciwon jiki ko gajiya ganin yadda jininsu ya motsa ko ina.
3: Shiga Rai: Maauran da suka saba da yin kafi shayi suna matukar kewar junansu a duk lokacinda guda yayi tafiya ko wata lalura ta gifta ba a samu yi ba.
Jima’i na Kafi Shayi yakan cusa kauna da soyayya a tsakanin ma’aurata. Jima’i ne mai shiga rai da ratsa zuciya.
4: Lafiyan Al’aura: Mazan masu saurin inzali sukan iya samun Karin lokaci na jimawa akan matansu a Jima’i na kafi shayi. Haka nan ma’auratan da suke burin haihuwa masana suka ce ciki na saurin shiga a wannan Jima’in na sanyin safiya.
Masana suka ce a wannan lokacin kwayoyin maniyi dana mace duk suna kwance cikin natsuwar yadda zasu iya samar da abunda ake bukata daga garesu.
5: Yarinta: Masana sukace muddin ma’aurata suna yawan yin Jima’in Kafi Shayi, da wahala tsufansu ko yawan shekaru su zai bayyana. A cewarsu masu yin wannan Jima’i suna mutuwa ne da kuzarinsu da kuma yarintarsu a fuska.
Ganin yadda wannan Jima’in yake da alfanu ga ma’aurata, da fatan zasu rika ganin kamin su sha shayi, to su soma yin abunda yafi shayin tukun.