Kalaman Soyayya

Abubuwan 5 Da Zasu Iya Faruwa Da Nonuwanki Yayi Kara Shekaru

Su dai nonuwa sunada matukar mahimmanci a wajen mata. Bayaga samar da abinci da nonuwan mata keyi, hallitar nonuwan mata na kara musu kyau na halitta da kuma bayyana tsarin kyau kwalliyar mace. Ta bangaren Jima’i nonuwan mace suna taka mahimmin rawa wajen motsa masu sha’awa da kuma baiwa mazajensu damar wasa dasu domin karin inganta wasannin motsa juna. Tonga Abdul tonga ne ya ruwaito.

Da wadannan ne mata suke burin ganin sun mallaki nonuwa tare da burin ganin cewa sun tsufa ko sun mutu da su.
Sai dai akwai wasu abubuwan da nonuwan na mata suke yi ko zama yayin da duk wata ‘ya mace take kara shekaru. Wadannan abubuwan kuwa sune:Abubuwan 5 Da Zasu Iya Faruwa Da Nonuwanki Yayi Kara Shekaru

1: Raguwa- A lokacin da mace take kara girma, wasu matan nonuwansu suna kara girma wasu kuwa suna kankancewa ne. Don haka idan naki na yin daya daga cikin wadannan abubuwan guda biyu. Masana sukace kada ki damu kanki daman haka abun yake.

2: Nankarwa- Akasarin mata idan suna kara shekaru nonuwansu na kara kara girma ko raguwa, a wannan yanayin ne kuma fatan jikin nonuwansu yayi nankarwa.

Ba kamar yadda wasu suke tunanin cewa duk wacce aka ga nonuwan ta yayi nankarwa ta taba haihuwa. Abun ba haka yake ba. Domin shi fatan mutum a lokacin da ya samu sauyi daga yadda yake dole zai tsage, hakan ne yake jawo nankarwa a jikin mutum.
Don haka idan kinga nonuwan ki sun yi hakan kada ki damu an samu sauyi ne daga girma ko raguwar da nonuwan naki suka yi.

3: Kuraje- Akan samu kuraje su fitowa nonuwan mace a lokutan da take kara shekaru. Wannan alamun inji masana yana bukatar mace tayi maza taje taga likita. A cewarsu kuraje suna daya daga cikin alamun kamuwa da cutar daji wato cancer na mama ga mata. Don haka duk wacce taga nonuwan ta suna yin hakan to tayi wuf taga likita.

4: Zubewan Nonuwa- Daya daga cikin abubuwan dake sa nonuwan mace su zube shine yawan shekaru bayan yawan haihuwa. Mace koda bata haihuwa idan shekarunta suka ja nonuwanta suna iya zubewa. Wannan kada ya saki tashin hankali ba matsala bace.
Sai dai da akwai hanyoyi na zamani dana gargajiyan da mata zasu iya amfani dasu domin su tsufa da nonuwansu.

5: Sakewar Kan Nonuwa: Shafin WebMD dake wallafa labaran kiwon lafiya suka ce yanayin nonuwan mace na soma sauyawa ne daga shekaru 30 da haihuwa. Hakan na faruwa ne saboda yadda sinadaren dake rike da nonuwan suke rage karfin su. Hakan kuma yasa sai aga kan nonuwan matan da suka nasu baida karfi kaman na masu karancin shekaru da za a ga sun yi baki sun yi tauri kuma sune a mike idan sha’awarsa mace ya motsa.
Don haka idan shekarunki sun ja kuma kika ga kan nonuwan ki niples sun baje, kada ki damu shekaru ne suka ja.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button