Labarai

Abubuwan da yake kawo mutuwae aure a kasar hausa

Me Ya Sa Auranmu Ke Yawan Mutuwa?

Mun dan yi wani bincike da mu ka gano wasu abubuwan da ke saurin kashe aure ko da maaurata suna son junansu, za mu fara dauko su daya bayan daya muna tattaunawa.

Abu na farko da ke cikin wannan rukunan da ke kawo matsaloli a zamantakewar auranmu (hausawa) har ya kai ga rabuwa shine rashin (communication), wato tattaunawa da fahimtar juna.

Kamar yadda muka sani shi aure wani abu ne da mutum biyu suka yi yarjejeniyar yin sa gami da amincewa za su zauna zama na har abada domin taimakon juna da samar da zuria masu inganci da kuma farin ciki tsakaninsu, da samun lada da rabautar da zata kai su har aljanna, don haka a irin wannan zama ba soyayya kawai ake bukata ba dole sai an samu fahimtar juna wanda shine abun da ya yi karanci a zamantakewar auranmu.

Misali sau da yawa namiji yana ganin matarsa tana aikata wani abu da ransa bai so ko ya shiga wani hali a kasuwa ko gurin aiko na damuwa, ko matar ta tsiro da wasu halaye da bai san ta da su ba, maimakon ya zaunar da matarsa su tattauna su gano bakin zaren sai dai ya tafi majalisa yana tattara laifi gaba daya yana dorawa mata ko ya samu abokinsa ko wasu yan’uwansa yana gaya musu matarsa kazama ce ko bata iya girki ba ko tana kaza da kaza, ko tunda ya fara samun matsala a kasuwancinsa ba ta daga masa kafa, bayan bai zaunar da ita sun tattauna ya gaya mata irin matsalar da ya ke fuskanta ko abun da ta ke masa da baya so ba.

Haka nan itama a bangaran mace idan ta ga mijinta ya sauya halaye ko ya tsiri wasu abubuwa ko ya daina yi mata bukatunta kamar yadda ya saba ko ya daina zaman gida ko daina cin abincinta ba za ta zaunar da shi su tattauna ta ji daga bakinsa ba sai dai ta je ta samu kawaye ko dangi tana gaya musu mijinta kaza mijinta kaza, duk da wani lokacin matan sukan ji shakkar tarar miji domin su tattauna matsalolinsu.

Wannan rashin tattaunawar tana kawo babban gibi gami da haifar da matsaloli a cikin aure, don haka ina kira ga magidanta musamman maza su koyi tattauna komai da iyalinsu ba dole sai ka gayawa matarka sirrinka ba (Wanda idan da hali ma yakamata ka fada saboda halin mutuwa) idan ka samu matsala gurin aiki ko kasuwanci zaunar da ita ka gaya mata wance yanzu kasuwa babu ciniki don haka zamu rage yin kaza da kaza, sannan idan kin ganni na dawo gida a fusace ko na sauya miki ki yi min uzuri domin na shiga wani hali, duk kuma wani bakon abu ko abun da baka so ya shigo gidanka ko ta sauya wasu dabi’u ko kawaye ko dai wacce irin muamala nuna mata gaya mata, insha Allah za ka ga an samu saukin fahimta, domin aure ya mutu da yawa akan kananan abubuwa ko kuma ma’aurata su zama makiyan juna babu gaira babu dalili saboda zato da zargin juna suna kuma kwana su tashi a gado daya su kasa tattaunawa.

A bangaran mace kema idan kin ga mijinki ya tsiri wasu halaye da ba ki saba gani ba zauna ki nutsu ki gane menene ya faru, shin ke kika sauya da yi masa wasu abubuwan ko a gurin aiki/kasuwa ne ya samu matsala, ko wata ce ya gani ta ke son kwace miki shi, idan kin gano ko baki gano ba zaunar da shi ku tattauna ku fahimci juna Insha Allah za a samu saukin damuwa.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button