Labarai

Yan sanda sun kama Mawaki Ice prince yayinda yayi yunkurin Garkuwa da Jami’inta

Rundunar ‘yan sandan jihar Legas ta kama shahararren mawakin nan na Najeriya, Ice Prince, bisa laifin cin zarafin wani jami’in dan sanda

An tattaro cewa da misalin karfe 3 na safiyar ranar Juma’a ne jami’an ‘yan sanda suka kama fitaccen mawakin nan Oleku crooer bisa laifin tuki ba tare da lacicin mota ba.jaridar dimokuraɗiyyar na ruwaito

Ice Prince wanda da farko ya amince a kai shi ofishin ba tare da bata lokaci ba, ya yi awon gaba da dan sandan a cikin motarsa, ya afka masa, sannan ya yi barazanar jefa shi a cikin tafkin.Yan sanda sun kama Mawaki Ice prince   yayinda yayi yunkurin Garkuwa da Jami'inta

Da yake tabbatar da kamun, kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Legas, SP Benjamin Hundeyin, ya ce an kama Ice Prince kuma za a gurfanar da shi a gaban kuliya a yau.

A cewar Hundeyin “Da misalin karfe 3 na safe @Iceprincezamani an dakatar da shi ne saboda tukin mota ba tare da lasisi ba Ya amince a kai shi ofishin ‘yan sanda.”

“Daga nan ne ya yi awon gaba da dan sandan da ke cikin motarsa, ya afka masa, sannan ya yi barazanar jefa shi a cikin kogin. An kama shi kuma yau za a gurfanar da shi a gaban kuliya.”

Majalisar Gudanarwa ta Jami’ar Jihar Gombe (GSU) a ranar Alhamis ta umurci dukkanin Ma’aikatan Makarantar da su koma bakin aiki cikin gaggawa.

Hakan na ƙunshe ne a cikin wata takarda ta cikin gida mai dauke da kwanan watan 2 ga watan Satumba mai dauke da sa hannun magatakardar jami’ar, Dr Abubakar Aliyu Bafeto.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button