Labarai

Yadda Maɗigo (lesbian) ke Neman cin ƴan matan Arewa da yaki

Koda yake ba yau na soma yin sharhi akan wannan lamari na Maɗigo ba, saidai a wannan karon nazo muku da wani ƙwarya-ƙwaryan bincike da muka yi haɗaka wajen gudanar dashi tare da yin sharhi na bai ɗaya dangane da wannan lamari daya yaɗu tsakanin Matan Arewa.

Mun gudanar da wani zuzzurfan bincike da nazari na musamman akan Matan Arewa ƴan Mata, Zaurawa da Matan Aure fiye da guda dubu biyu da ɗari huɗu da sittin da biyu (2,462).Yadda Maɗigo (lesbian) ke Neman cin ƴan matan Arewa da yaki

Mun gudanar da wannan bincike ne ta dandalin sadarwa daban-daban na Yanar Gizo kama daga kan What’sapp, Facebook da Instagram inda muka gano fiye da kaso arba’in 40% cikin ɗari 100% na Matan da muka bibiya Hausawa ne kuma mafi yawanci ƴan Mata ne da basu taɓa Aure ba wanda aka yaudari tunanin su suka shiga cikin wannan harka ta Maɗigo (Lesbian).

Bayan bin diddigi da nazarin rayuwar waɗan nan ƴan Mata munyi fargabar cewa akwai yiwuwar Jihar Kano ta zamo ta ɗaya (1st) dake da kaso mafi yawa na ƴan Mata da Matan Aure ƴan Maɗigo a faɗin Arewacin Najeriya duba da yawan Matan ƴan asalin Jihar Kano da muka ci karo dasu suna wannan harkar.

Shin menene musabbabin yaɗuwar Maɗigo a yankin Arewacin Najeriya?

Gaskiyar magana akwai hanyoyi da dama dake da nasaba da yaɗuwar harkokin Maɗigo a yankin Arewacin ƙasar nan, saidai mun fi karkata hankalin mu akan wasu abubuwa da muke ganin sune ummul aba’isin yaɗuwar wannan Fasiƙanci a yankin Arewa.

NA FARKO! SHAGULGULAN BIKI KO PARTY..

Yana daga cikin manya-manyan hanyoyin da ƙungiyoyin Maɗigo na Duniya ke bi wajen yaɗa ayyukan su a faɗin Duniya wato shirya shagulgula da sharholiyar sheɗanci.

Haƙiƙa wannan ɗabi’a da aka bijiro da ita cikin al’ummar Hausawa na shagulgulan biki da casun Party mafi yawancin lokuta a cikin ɗakunan taron bukukuwa na Event Center a turance suna da nasaba wajen buɗewa Mata ƴan Maɗigo ƙofar shiga jikin ƴaƴan Hausawa su koyar dasu wannan mummunar ta’ada tasu.

Ko ban faɗa ba dani daku muna ganin yadda taruka a gidajen casu (Event Center) yake sauya salo da tunanin ƴan Matan Hausawa daga Al’adu da shiga irin ta Malam Bahaushe zuwa shiga irin na rashin tarbiyya da zubewar kima da Mutuncin al’ummar Hausawa.

Abin lura shine ganin yadda yayin gabatar da ire-iren waɗancen shagulgulan ƴan Matan Hausawa ke yin ɗinke-ɗinke na rashin Ɗa’a tare da yin raye-raye na rashin kima a gaban Iyaye da dangi da sauran mahalarta taron batare da nuna kunya irin ta Hausa Fulani ba.

To a irin wannan lokutan na shagulgulan biki ko Party Mata ƴan Maɗigo kan samu dama wajen ƙulla ƙawance da ƴan Matan da suka lura ruwan su isa wanka inda daga bisani suke amfani da ƙwarewa wajen shawo kansu har su kai ga shiga wannan harka ta Fasiƙanci.

NA BIYU! SHAFUKAN YANAR GIZO (INTERNET)..

Har’ila yau a cikin jerin binciken mu, a iya Manhajar Facebook kaɗai mun gano Mata guda dubu biyu da ɗari ɗaya da sha takwas (2,118) dake da alaƙa da harkokin Maɗigo kuma kusan dukkan su Hausawa ne daga Jihohin Arewacin Najeriya.

Daga cikin su guda ɗari shida da tamanin da huɗu (684) Matan Aure ne, sai guda ɗari huɗu da takwas (408) Zaurawa, sai ragowar guda dubu ɗaya da ishirin da shida (1,026) wanda sun kasance ƴan Mata ne kamar yadda kowacce ta bayyana a Profile Info ɗin ta, da kuma waƴanda muka bi diddigi muka tabbatar da haka.

Domin kore shakku akwai ƴan Mata sama da guda ɗari (100+) da Matan Aure sama da guda ishirin (20+) daga cikin waɗanda muka bibiya yanzu haka a cikin jerin Firends ɗina na facebook kuma muna da cikakkiyar shedar cewa suna da alaƙa da harkar Maɗigo.

Koda yake hakan bazai shafi alaƙa ta dasu ba domin yanzu haka ina zantawa da wasu daga cikin su kuma ina samun wasu bayanan sirri, harma nakan leƙa Groups ɗin su a wasu lokutan domin samun bayanan da nake nema.

Daga cikin bayanan da nake samu a wajen wasu ƴan Mata wanda suka tsinci kansu cikin wannan harka kuma suke neman hanyoyin da zasu bi domin barin ta, na samu bayanai akan shafukan sirri na ƴan Maɗigo sama da guda arba’in (40+) a wannan dandalin na Facebook.

Kuma hakan ya sake tabbatar min da nagartar binciken mu wanda muka yi ƙiyasin cewa akwai shafukan sirri na ƴan Maɗigo mai tarin yawa a Facebook inda wasu da dama ke fakewa da tallan kayan Mata suna yaudarar su zuwa harkar Maɗigo.

Daga cikin ire-iren waɗan nan shafuka kusan kaso sittin 60% cikin ɗari 100% mallakin ƴan Maɗigo ne, haka nan mabiyan su kusan duk ƴan matan Arewa ne da Samari Kawalai wato masu haɗa Kasuwanci na Zinace-Zinace ta Yanar Gizo (Sex Connection).

NA UKU! AMFANI DA KAYAN MATA..

Idan aka ce kayan Mata ana nufin magungunan gargajiya ko (Herbal Medicine) da Matan Aure ke amfani dasu na gyaran Jiki a wasu lokutan harda mallake Mazajen su.

To a wannan Zamanin ba kawai Matan Aure ne ke amfani da kayan Mata ba, binciken mu ya gano yadda da yawa ƴan Matan Arewa ke amfani da ire-iren waɗan nan magunguna batare da sunyi koda Auren fari ba.

Saidai hakan nada nasaba da Iyayen su Mata domin da zarar ƴaƴan su sun Balaga sai su yaye musu Hijabi su dinga bayyana musu wasu sirrika na Auratayya tare da ɗora su akan magungunan Mata batare da tunanin irin hatsarin dake tattare da amfani da magungunan ga Macen da batayi Aure ba alhali tana Balagaggiya.

To da zarar Yarinya ta sha wancan tayi matsi da wancan sai tunani daban-daban na buƙata su dinga bijiro Mata wanda a irin wannan yanayi da dama Yan Mata basu fiye jurewa ba har hakan kansa su soma jarraba ɗabi’ar nan ta biya wa kai buƙata wato Istimna’i (Masturbation) da hannu ko wani abu makamancin haka domin samun biyan buƙata.

Wannan bincike ne da muka gudanar akan Mata da yawa musamman ƴan Mata kuma tabbas muna da tabbaci da yawa yan Mata a wannan Zamanin suna aikata Istimna’i (Masturbation) harma sukan kira Samarin su a waya domin suyi musu zantuttukan Batsa (Sex Chat) ta yadda zasu samu nishaɗi yayin da suke yin Istimna’in domin hakan rage wa kai raɗaɗin sha’awa ne a wajen su.

Saidai a nazarin binciken mu mun gano yin Istimna’i (Masturbation) ga ƴa Mace na ɗaya daga cikin somi-somin shiga harkar Maɗigo gareta kasancewar duk wadda ke wasa da kanta bata fiye bijirewa yayin da ƴar uwar ta Mace ta nemi yin wasa da ita domin biyan buƙata ba.

Dan haka amfani da kayan Mata ga Mace Budurwa ba daidai bane matuƙar idan zai iya tara Mata sha’awa a marar ta da sunan ƙarin Ni’imah, dan haka Iyaye Mata ku kiyaye da irin magungunan da kuke shayar da ƴaƴan ku.

NA HUƊU! MAKARANTUN ZAMANI..

Mu lura ƴan Mata kanyi ƙawaye daban-daban a Makaranta saidai mafi yawanci ƴan Matan suna ƙulla ƙawance da ƴan Maɗigo a Makarantun kwana ko manyan Makarantu na Jami’a batare da sun fahimci hakan ba.

Koda yake da yawa ƴan Matan dake Makarantun kwana sukan yi harkokin Maɗigon su ne a cikin Makaranta kodai a ɗakunan kwanan su ko banɗaki ko a wasu keɓantattun waje na cikin Makaranta domin yana wahala su haɗu idan ba’a cikin Makaranta ba.

Su kuwa ƴan Matan Jami’a kan ƙulla ƙawance har sukai ga ziyartar gidajen juna tare da fice-ficen zuwa unguwa, yau ana gidan su wance gobe a nufi gidan su wance.

Girman ƙawancen su kansa su ƙirƙiri wasu Groups na Chatting mafi yawanci a manhajar What’sapp inda a ciki suke tattaunawa da juna tare da nishaɗantar da juna a wasu lokutan sukan haɗa casu (Party) ko Get Together cikin salo na abota.

A lokutan gudanar da Shagulgulan sukan bayyana irin kayan da suke buƙatar kowacce tasa wanda a mafi yawanci riga ƴar kanti ce (T-shirt) da wando ɗan kanti ko buje (Jeans – Skirt) wanda mafi yawanci suke matse jikin su dukkan Diri da Surar su ta bayyana.

To saidai masu yin Maɗigo a cikin su kanyi amfani da wannan dama wajen jan hankalin wasu daga cikin ƴan Matan zuwa Group ɗin su na zallar ƴan Mata masu harkar Maɗigo domin a duk lokacin da Mace ƴar Maɗigo taga Mace mai kyakkyawan Diri hankalin ta kan tashi harma taji Sha’awar haɗa mu’amula da ita.

Dan haka a ɓangaren Makarantu musamman Makarantun kwana akwai matuƙar wahala shawo kan lamarin, saidai muna kira ga Iyaye ya zamo wajibi garesu susa ido akan irin ƙawayen dake ziyartar ƴaƴan su da kuma irin fice-ficen da suka dace su dinga yi tare da ƙawayen su.

Idan bai zama wajibi ba zaifi kamata ƴaƴan ku Mata suyi Karatu a gaban ku, a ɓangaren Karatun Jami’a kuwa zaifi kyau kuyi musu Aure, idan Mijin su na da ra’ayi suyi Karatun Jami’ar a gidan shi yafi.

NA BIYAR! SHAFAR AL’JANNU..

A wani abu mai kama da ban mamaki game da Mata ƴan Maɗigo shine, da yawan su suna da matsalar shafar baƙin Al’jani mai hana ƴaƴa Mata Aure.

Wannan ne yasa mafi rinjaye na ƴan Maɗigo Mata ne wanda basu taɓa yin Aure ba (Ƴan Mata) kasancewar Al’janin yana cire musu Sha’awar yin Aure amma fa idan sun kwanta bacci suna yin mafarki ana Saduwa dasu inda a wasu lokutan tunanin irin wancen mafarkin kanzo musu a rai har Sha’awar su kan motsa wanda hakan kan jefa su aikata Zina ko Maɗigo ko Istimna’i domin samun sauƙin sha’awa, amma fa duk da haka idan wani yazo musu da batun Aure ba zasu amince ba.

A wasu lokutan kuma Al’janin kan haddasa musu sha’awa mai ƙarfi ta yadda zasu buƙaci Aure amma da zarar sun samu wanda ya tsaya da gaske zai Aure su sai maganar ta lalace, to suma irin waɗan nan ƴan Matan sukan kasa jurewa har sukai ga shiga harkar Maɗigo ko Zinace-Zinace da Samari domin samun sassauci.

Da dama daga cikin ire-iren waɗan nan Matan dake jimawa babu Aure ƙawayen su ƴan Maɗigo kan yaudare su suna faɗa musu cewa zasu samu biyan buƙata cikin sirri batare da ansan me suke aikatawa ba, kuma babu fargabar ɗaukar ciki tunda bada Maza suke Saduwa ba wanda hakan kanyi tasiri a zukatan su har sukai ga shiga harkar.

Abin lura shine koda babu shafar Al’jani mafi yawanci na ƴan Matan dake harkar Maɗigo suna da tsananin Sha’awa, hakan yasa suke gwammacewa suyi Maɗigo da ƴan uwan su Mata fiye da yin Zina da Maza domin gudun ɗaukar Ciki kuma hakan kan samar musu cikakken sirri kasancewar ba’a fiye zargin Mata idan suna shige da ficen su ba.

Gaskiyar lamari shine a halin yanzu muna cikin fargabar a cikin kowane rukunin ƴan Mata guda goma (10) akan iya samun ƴan Mata guda huɗu (4) wanda basu taba yin zina da namiji ba amma suna yin Maɗigo (Lesbian).

Yawancin Mata ƴan Maɗigo suna da kyawun fuska sannan suna da Diri da yalwar Sura kasancewar suna amfani da kayan Mata na gyaran Jiki kodan saboda su zamo abin sha’awa ga sauran abokan harkar su.

Har yanzu muna kan nazari da bincike akan wannan lamari na Maɗigo kasancewar kullum sabbin hanyoyi suke daɗa ɓullo dasu.

Alhamdulillahi wasu daga cikin waɗanda nake zantawa dasu sukan faɗa min cewa a shirye suke dasu daina wannan harka muddin suka samu Mijin Aure.

Anan zan dasa aya da fatan Allah ya dubi lamarin ƴan uwan mu Mata musamman na nan Arewacin Najeriya, ya yaye musu wannan masifar data ɓullo cikin su.

Ya Allah ka shirya masu yin wannan harka ka ganar dasu gaskiya, ka kare waɗanda basu shiga cikin ta ba, mu kuma da muke ƙoƙarin ceto al’ummar Annabi ya Allah ka bamu kariya da ƙarfin gwuiwar cigaba da yaƙar duk wani abu daya saɓa da Addinin ka.

Allah ka gafarta mana baki ɗayan mu!

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button