Yadda ƴata ummi ta rasa ransa a hannun saurayinta – Inji mahaifiyar ummi
A safiyar yau mun tashi da wanni mummunan labari wanda wata budurwa ta rasa ranta ga wani dan kasar china kamar yadda shafin Labarunhausa na ruwaito.
Daily Trust ta ruwaito yadda aka kashe wata matashiya a unguwar Janbulo Quarters da ke karamar hukumar Kumbotso a jihar Kano a daren Juma’a.
Marigayiyar, wacce aka fi sani da ‘Ummita’ ta yi makarantar koyon aikin jinya da ungozoma a Kano. An yi jana’izar ta da misalin karfe 10 na safiyar ranar Asabar, kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.
Da take magana kan lamarin, mahaifiyar ta bayyana cewa, “Saurayin Ya kasance kullum yana zuwa yana son ganinta ‘yata ita kuma ta ki. Wannan karon da ya zo sai ya yi ta kwankwasa kofa. Da na gaji da jin bugun kofar sa,sai na bude kofar ko da na bude sai ya tura ni gefe ya shiga ya fara daba mata wuka.
“Na fara ihu mutane suka taho a guje.Koda Muka garzaya da ita asibiti kafin mu isa ma ta rasu. Hakan ya faru ne da misalin karfe 9:30 na dare. Muna gida da kannenta biyu a lokacin da abin ya faru. Yayanta yana waje mahaifinta ya rasu. Ana ruwan sama a lokacin, mutane suna cikin gida shiyasa ba su ji ihu na ba sai da wani ya zo ya yi ƙoƙari ya shiga ta taga.
“Ina son hukumomi su shiga wannan lamarin. Sun dade da rabuwa. Har ta yi aure amma daga baya auren ya rabu. A lokacin ne ya dawo rayuwarta, yana matsawa dole sai ya gan ta. Ya na zuwa gidan mu kullum duk da ba mu so amma yaki ya gane. Mun yawan koranshi. Lokacin da na yi ƙoƙarin sanar da ’yan sanda, ’ya’yana suka hana ni.
“Mutumin da ya zo taimakonta ta taga ya shiga; shi ne ya kama shi ya fito da shi. Ya gudu sukayi kamo shi. Yanzu yana hannun ‘yan sanda. Ita ce babbar ’yata mace amma tana da ’yan’uwa maza biyu.
Ya fahimci cewa ba ta son ganinsa. Idan ya kira, ba ta ɗauka. A lokacin ne ya yanke shawarar abinda ya aikata. Kusan awa daya yana buga kofar. Ita ce ta ce in je in sallame shi bayan na bude gate ya ture ni.
“kai tsaye dakinta ya nufa. Ya san inda dakin yake domin ya saba shigowa, a mafi yawan lokuta, dan uwanta ne ke kora shi. A Shoprite suka fara haduwa a lokacin da ta je siyan turare suka yi musayar lambobin waya. A haka suka fara kiran waya.
“Lokacin da ta yi aure, sun rabu har sai da ta rabu da. Mijinta ya yi zargin suna hira da shi ta waya duk da cewa ba hakan ne ya janyo lalacewar aurenta ba. Tabbas ta gaya masa cewa za ta aure shi, amma da yake waliyanta sun hangi matsala sai suka ki, amincewa ni ma kuma na yadda da haka.”