Labarai

Wata Mata Mai Kimanin Shekaru 70 Tace Ta Shirya Aure Kuma Ita Sabuwace Fil A Leda

Wata Mata Yar asalin Kasar Congo yace yanzu haka tana maraba da dukkan Namijin daya shirya Auren ta, Matar wacce yanzu haka take cika shekaru 70 a duniya.

Matar Mai suna Alphonsine Tawara, tace Maza da dama sun nemi Auren ta lokacin tana da kuruciya, Kuma tayi soyayyah mai tarin yawa sai dai a lokacin mata bukatar Aure.shafin Dimokuradiyya na ruwaito.

Ta dauki hukuncin rashin yin Aure ne da wuri a kokarin ganin ta samarwa Yan’uwanta Karatu ingantacce.

Malamar Makaranta ce ta kwashe shekaru Mai tsawo tana karantar, bata da Yaro ko guda amma dalubanta suna kwashe mata kewar rashin Yaranta na Jini.

Yanzu haka tana neman Mijin Aure sai dai abun yana nema ya gagara, amma tana mai tabbatarwa da dukkan Wanda zai Aure ta zai same ta Sabuwa fil a leda kamar Budurwa.

 

WANI LABARI: Layin wutar lantarki na ƙasa ya sauka gaba ɗaya

 

Layin wutar lantarki na ƙasa ya sauka gaba ɗaya, inda ya zama babu megawatts (MW) ko ɗaya, tun da karfe 10:51 na safiyar yau Litinin, lamarin da ya janyo katsewar wutar lantarki a fadin kasar baki daya, inji rahoton Daily Trust.

Wannan ci gaban ya faru ne kwanaki kaɗan bayan masu amfani da wutar lantarkin wutar ta samu sosai a ƙasar.

Tashar wutar lantarki ta kasa da misalin karfe 10 na safiyar yau Litinin ta samu megawatt 3,712 da aka samar daga kamfanoni 21 na rarraba wutar lantarki (GenCos) kafin ta koma 0MW bayan awa daya.

Bisa ga bayanin da aka samu daga tumbin yaɗa bayanai na wutar lantarki, wani sashe na Kamfanin Rarraba Wutar lantarki (TCN), Afam IV ne kawai a kan layin wutar, amma ba tare da an samu komai na wutar ba har zuwa karfe 12 na rana.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button