Wata Budurwa Ta Kashe Dubu 9 Kuɗin mota Domin Ganin Saurayin Da Suka Haɗu A Midiya
Wata ƴar Najeriya ta yi kuka bayan ta kashe N9k a sufuri domin ganin saurayinta, yayin da shi kuma ya ba ta N1,300 bayan sun shafe kwanaki uku suna lalata.
Kafofin sada zumunta sun yi ta ce-ce-ku-ce tun bayan da wata ƴar Najeriya ta bayyana abin da ya faru da wani saurayi da ta je Legas domin ta ganshi wanda suka haɗu a soshiyal midiya.
A cikin sakon imel da matar ta aika wa ƙwararre kan hulɗar dangantaka, Joro Olumofin, ta bayyana yadda ta haɗu da wani saurayi a Instagram bayan alaƙarsu ta yi tsanani kuma suka yanke shawarar haɗuwa.
Ta bayyana cewa ta kashe N9k ne kuɗin sufuri har zuwa Legas domin ganawa da shi tare da yi mata alƙawarin ba ta kuɗi da kuma kwamfutar tafi-da-gidanka da saurayin ya yi mata.
Wani labari : Masu Garkuwa Da Mutane Sun Sace Mutane Da Dama A Jihar Sokoto
Jiya da misalin ƙarfe ɗaya na dare wasu mutane da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun shiga unguwar Moreh dake cikin ƙaramar hukumar Kware a jihar Sakkwato sun sace wasu mutane da dama har da wata baiyar Allah wacce take shayar da jariri ɗan wata shida da haihuwa.
Ita wannan baiwar Allah mai suna Maryam Ahmad sun umurce ta ne da ta ajiye jaririn kafin nan suka tafi da ita.
Kafin faruwar hakan mazauna Unguwar sun daɗe suna zargin wasu mutane dake zaune a gidajen hayar unguwar wadanda suke kyautata zaton barayi ne amma ba su sanar da hukumomin tsaro ba.
A haka nake ƙara kira da jan hankali ga al’ummar kowanne yanki cewa su ringa bincike da la’akari ga wadanda ake baiwa gidajen haya a cikin unguwanni domin kaucewa ire-iren faruwar hakan.
Muna rokon Allah ya bayyanar da wadannan bayin Allah.