Wasu Daga Cikin Jaruman Da aka cire yayin da aka shafe fuskokin wasu A Cikin Shirin Labarina
Wadanan sune kadan daga cikin fuskokin da anka cire a cikin shirin labarina mai dogon zango wanda shafin dimokuraɗiyya na wallafa a shafin na Facebook.
1-Ibrahim Mandawari
Tun da farko Jarumi Ibrahim Mandawari ne aka fara yin waje da shi a cikin shirin LABARINA mai dogon zango, idan baku manta ba shine ya fara fitowa a matsayin Mahaifin Presidor, kafin daga bisani aka cire shi aka sauya da Jarumi Tijjani Faraga, kuma har yau babu cikakken dalili.
2-Nuhu Abdullahi
Nuhu Abdullahi wanda aka aka fi sani da Mahmoud a cikin shirin, shine na biyu a cikin Wanda aka cire a cikin shirin na LABARINA, Rahotanni sun tabbatar da cewar matsala aka samu hakan ta saka dole aka lauya alkalami aka ce Mahmoud ya Mutu ba don ana so ba.
3-Lailah
Maryam Waziri, ita ce ta uku data fita a cikin shirin LABARINA sakamakon Aure data yi a Jihar Kaduna, sai dai kwata kwata labarin bai sake bi ta wajen ta ba bare a iya ganewa ko zaa iya sauya ta da wata, kuma har yanzu masu shirya shirin basa amsa tambaya a kan haka.
4-Nafisa Abdullahi
Nafisa Abdullahi, wacce aka fi sani da Sumayya a cikin shirin, wanda ita ce tauraruwa mai haske, sai da aka kusa yin Uwa-Uban ka da ita kafin ta rubuta takardar yin Murabus, an danganta cire kanta data yi a cikin shirin da samun wata hatsaniya da Nazir Sarkin waka, wasu hujjojin Kuma sun bayyana cewar kan batun bayar da kudin aiki ne sarkin waka yayi mata ba daidai ba a saboda haka aka yi baran-baran.
5-Halima Atete.
Tun bayan da aka fara haska sabon Shirin baa sake ganin Halima Atete a cikin shirin ba har ma ake tunanin an sauya ta da wata Jaruma Mai suna Hajara Mai wushirya, tana nan a cikin shirin.
6-Garzali Miko
Garzali Miko wanda aka fi sani da Habu, a cikin shirin an dauki dogon lokaci baa sake ganin shi a cikin shirin ba, kuma an tabbatar da cewar baza a sake ganin shi a cikin shirin ba.
7-Mai Kemis.
Dambaza’u, ya fito a cikin shirin wanda sune taurarin farko-farko a cikin shirin na LABARINA amma sauya akalar rubutun shirin ya saka dole aka goge babin su.
8-Malam Aminu Saira.
Daraktan Shirin Malam Aminu Saira, shima yana daga cikin jaruman farko-farko a cikin shirin, idan baku manta ba shine ya fara fitowa a matsayin direban Baban Presidor, a farkon Shirin Ibrahim Mandawari ne Baban Presidor kafin daga bisani aka sauya da Tijjani Faraga.
9-Dija
Hafsat Idris, wacce ake yiwa lakabi da Barauniya, tayi shura a cikin shirin kuma ana kiran ta da Dija, salon rubutun labarin ya saka dole aka shafe fuskar ta a cikin shirin ba don ana so ba.
Sauye-sauyen da aka sami a cikin shirin ya saka wasu na ganin cewar yanzu shirin bashi da alkibila, yayi da wasu suke cewar yanzu ne ma Shirin yake daukar seti.