AddiniLabarai

Sarkin Kano Ya Naɗa Sheikh Daurawa A Matsayin Babban Limami

Advertisment

A safiyar yau Alhamis, 15-9-2022 Mai Martaba Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero, ya naɗa babban malamin addinin Musuluncin nan, Assheikh Muhammad Aminu Ibrahim Daurawa, a matsayin babban limamin sabon masallacin jami’ar Skyline da ke tsohon ginin dogon bankin a kusa da sakatariyar Audu Baƙo da ke Kano.

Bikin naɗin da aka yi shi a fadar Mai Martaban ya samu halartar manyan jami’ai na fadar Mai Martaba San Kanon.

Daga isar shi fad’ar, Sheikh Malam Aminu Daurawa ya zarce ya gaida sarki, sannan ya yi wa sarki addu’ar fatan alheri da fatan zaman lafiya ga al’ummar jihar Kano, da ma ƙasa bakiɗaya.

A wani abu da ba a saba gani ba a fada sosai, sarkin ya buƙaci su gaisa da malam Daurawa, inda kuma ya yi addu’a ta musamman tare da yabawa Shehin Malamin game da ƙoƙarin wayar da kan mutane zuwa ga tafarkin Allah.

Advertisment

“Muna ganin irin abubuwan da malam yake yi na wayar da kan al’umma da nusarwa. Muna yi wa Malam godiya da addu’ar fatan alheri. Muna ganin bidiyoyi na karatuttuka iri-iri, Allah Ya saka da alheri.” Inji mai martaba sarki.

Haka kuma bayan an naɗa Malam tare da na’ibansa guda uku, a masallacin fadar Sarkin Kano, tawagar Malam Aminu Daurawa sun dawo domin sake yi wa mai martaba sarki addu’ar fatan alheri.

A karo na biyu bayan naɗin, sarki ya ce a gaya wa Malam Aminu Daurawa lallai malafar da aka ɗora masa ta dace kuma ta yi kyau. Wannan ya sa aka yi dariya tare da murna a cikin fadar ta Kano.Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa

Wakilin TDRHausa ya tabbatar da cewa an ga alamun farin cikin da walwala a fuskar Mai Martaba sarkin Kano da shi kansa Shehin Malamin, Malamin Aminu Daurawa a yayin wannan naɗi.

Bayan an naɗa wa Sheikh Daurawa rawani, an sanya masa alkyabba, sannan aka sanya masa malafa aka ba shi sanda, sannan kuma aka yi masa addu’ar fatan alheri.

Sauran waɗanda mai martaba sarkin ya naɗa, a matsayin na’iban Malam Daurawa sun haɗa da Dr. Jamilu Lawan Ajiya Fagge, daga jami’ar DutsinMa, a matsayin na’ibi na ɗaya. Sai Malam Anas Muhammad Madabo, a matsayin na’ibi na biyu. Sai kuma Dr. Muhammad Sulaiman Abdullahi, daga jami’ar Bayero, a matsayin na’ibi na uku.

A lokacin da ake karanta takardar babban limamin Kano a bisa gwajin da aka yi wa Sheikh Daurawa da na’iban nasa, Farfesa Emeritus Sani Zahraddin ya bayyana cewa lallai Malam Aminu Daurawa yana ƙoƙari wajen faɗakar da al’umma da kuma nusar da su zuwa kan hanya tagari.

Sai dai a yayin jawabin farfesan, ya nemi malam da ya ja hankalin limamin masu tsawaita sallar Juma’a, har a yi minti 40 ko ma sama da haka ana huɗuba. Ya bayyana cewa lallai mafi kyawun zance shi ne wanda aka yi shi ɗan kaɗan, kuma ya zamo mai tarin ma’ana. Sannan ya ƙara da cewa ya kamata limamin su sani, a cikin masu bin su salla, akwai masu rauni da marasa lafiya da masu wasu buƙatun na daban.

An yi wannan bikin naɗi lafiya cikin farin ciki da annashuwa.

Daga Ibrahim Mukhtar

Advertisment








Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisment
Back to top button