Labarai

Kotu ta aike da Kansila ɗan shekara 58 gidan yari a Kano

Kotun majistare, mai lamba 61 da ke zaman ta a unguwar Mariri a Kano, ƙarƙashin mai Shari’ah Salisu Idris Sallama, ta aike da wani kansila, Maigida Sani, ɗan shekara 58, zuwa gidan gyaran hali sabo da kasa cika sharuddan beli.

Daily Nigerian Hausa ta jiyo cewa an gurfanar da Kansilan, wanda ɗaya ne daga cikin kansilolin Karamar Hukumar Kura, a gaban kotun bisa zargin sa da laifin zagin cin mutunci, ɓata suna, kalaman tinziri, da bayanan ƙarya, harma da maganganu masu haifar da rashin zaman lafiya ga shugaban Karamar Hukumar Kura, Mustapha Abdullahi.Kotu ta aike da Kansila ɗan shekara 58 gidan yari a Kano

Bayan da mai gabatar da ƙara, Barista Mahadi ya karanto kunshin tuhumar da a ke yi wa Sani, nan take ya musanta dukkannin laifukan da ake zargin sa dasu.

Hakan ne ya baiwa Mahadi damar sa ke ɗaukar wata rana domin sake gabatar da Kansilan a gaban wannan kotu, inda nan take kuma kotun ta sanya ranar 22 ga watan Satumba domin dawowa kotun don ɗorawa daga inda kotun ta tsaya.

Sai dai a karshe kotu ta bada belin Kansilan, bisa sharuɗɗan kamar haka; mutane 2 zasu tsaya masa 1, limamin masallacin Juma’a, 1 kuma ya kasance mutum mai kamala, sannan za su ajiye hotunan su guda 2.

Ɗan sandan kotu zai je ya gano gidajen su, kuma za’a ajiye kudi a kotu naira dubu 200, a karshe kuma za su cike takardar rantsuwa a babbar kotun jiha wacce ta ke nuna kadarorin da su ka mallaka.

Daga nan ne sai ADC Musa Yola, jami’in gidan yarin ya tisa keyar Kansilan zuwa gidan yarin domin cika umarnin kotu, har sai wanda a ke ƙara ya cika ƙa’idojin beli.

Wani Labari:Fashewar tukunyar gas ta jikkata mutane 5 da kona gidaje da shaguna 17 a Jigawa

 

A ƙalla mutane biyar ne su ka ji raunuka daban-daban ‘, yayin da gidajen mutane da Shaguna suka ƙone biyo bayan fashewar wata tukunyar gas a Ƙaramar Hukumar Babura, jihar Jigawa.

Kakakin rundunar tsaron Sibil Defence (NSCDC) reshen jihar Jigawa, Adamu Shehu, ya tabbatar da faruwa lamarin a wata sanarwa da ya fitar da safiyar Talata.

Yace lamarin ya faru ne lokacin da wata babbar Motar dakon kaya maƙare da Tukunyar Gas ta yi bindiga a garin Babura.

Kakakin NSCDC yace Gidaje da yawa da shagunan al’umma sun ƙone sakamakon faruwar lamarin, inda ya ƙara da cewa mutane da dama sun jikkata, amma har yanzu ba bu wanda ya mutu.

“Mummunan lamarin ya auku ne jiya da daddare, ranar Litinin 12 ga watan Satumba, 2022 da misalin ƙarfe 9:00 na dare,” Inji shi.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button