Kalli Shirin LABARINA Season 5 Episode 1
Labarina shiri ne mai dogon zango wanda kuma ya samu karbuwa sosai a wajen mutane wanda gidan talabijin na arewa24tv ke haskawa a duk bayan sati daya wanda ake sanyawa ranar juma’a da misalin karfe takwas tun daga zango na farko har zuwa zango na hudu.
A yau kuma an sake dawowa tafiya dogon hutun da ankayi bisa tsayawa aikin wannan shirin tare da maye gurbin wasu jarumai da bazasu sake haskawa a fim din ba duba da kwantaraginsu ya kare.
Wanda a yanzu dai babu jarumi Nuhu Abdullahi wanda ake kira da suna Mahmud a cikin wannan shirin yayin da ita kuma Nafisa Abdullahi ake kiranta da summaya wanda sun taka rawar gani sosai a cikin wannan shiri.
Labarina fim ne da ya samu masoya sosai wanda kuma yanzu haka an maye gurbin Nafisa Abdullahi da fati washa wanda zata hau sunan Summaya.
Wanda kuma shi Mahmud daman an riga da an kashe shi tun cikin zango na hudu wato season 4.
Zaku ga irin yadda za’a fafata tsakanin presido da kuma Lukman wajen takarar neman auren Summaya wanda kuma akwai gwagwarmayar tsakanin presido da Baba Rabe duba da shine mahafin sumayya ya keta masa haddi yaci mutuncinsa a zama da sunkayi a gidan gyaran hali a duk a cikin shirin Labarina.