Addini

Huduba Mai zafi akan Waƙar CHASS ta Ado Gwanja – Dr Abdallah G/kaya

As sheikh abdallah usman Gadon kaya a cikin Hudubar ta wannan sati yayiwa mawakin nan mai suna Ado Gwanja nasiha irin ta addini Musulunci da jawo hankalin domin kuwa shi ne Musulmi ne har yanzu akwai hanyar tuba a wajensa.

As-sheikh Dr Abdullah Gadon kaya a cikin wannan hudubar da ya gabatar a jiya juma’a yayi kalamai da nasiha zuwa ga wannan matashin mawakin wanda yana da kyau mu kawo domin kowa ya saurara yaji domin wata Allah nasihar taje masa mallam yana cewa

Yanzu wannnan waka da ankayi a garin nan wani bawan Allah ake ta tada kura a garin nan,yanzu musulmi ya kamata yayi wannana abu?.

Dan musulmi wanda ya tashi a cikin musulmai wakoki na tada sha’awa na fitina yara kanana suna koya yarinya ta sun kuya ana sosa mata ,wai asosa la’illahah illalah balagaga,balagage kuma wai baza’a yi magana ba mutane sun kama baki sunyi shiru.

“Malam ya kara da cewa wajibi wannan ya tuba tunda musulmi ne wajibi a jawa wanda yayi wannan wakar kunne da wanda yayi da wanda zaiyi nan gaba.

Allah ya karawa hukumar tace finafinai albarka da take kokari wajen kare tarbiyya mutane kano da musulunci kuma wajibi ne mu taimake su wallahi.

Idan sunyi ba daidai ba muna sunkar idan sunyi daidai mu taimake su bai dace mu bari ana yakar su ba, musulunci suke taimaka Addini suke taimaka tarbiyya suke taimaka yara suna ta faduwa jarabawa amma duk sun iya waka yanzu Yanzu duk sun haddace waka cewa kake rubuta musu ankayi suka haddace a tafima anji ana sauraren wakokin amma sai azo ana koyawa mutane batsa.

Idan yan india sun yi ko yan amerika sunyi bamuda ikon da muyakisu ba yan garinmu bane ba yan addinmu bane ,amma dan harshenmu bazamuyi magana ba mu zuba ido muyi shiru bazamuyi nasiha ba a’a ba daidai bane.

Zaku saurari sauran bayyani a cikin wannan faifan bidiyo daga bakin shehin malamin Dr.Abdallah Usaman Gadon Kaya.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button