Labarai

Daman ba iya mai juna biyu nankarwa ke fitowa ba?

Duba Abubuwa 10 Da Suka Kamata Ka Sani Game Da Shafin lafiya uwar jiki na wallafa

1. Nankarwa alama ce ta talewar fata. An fi ganinta galibi a tsatstsaye a kan fata. Kalar nankarwa ya dogara ga kalar fatar mutum.

2. Akwai shimfiɗu uku da suka haɗu suka samar da fata. A likitance, nankarwa na faruwa sakamakon talewar shimfiɗar fata ta biyu.

3. Galibi ta fi fitowa a kan fatar ciki. Sai dai wasu lokutan tana bayyana a kan fatar cinyoyi, nonuwa, ƙugu, damatsa da sauransu.

5. Nankarwa aba ce ruwan dare. Kuma tana iya fito wa kowa, maza da mata, babba da yaro, ba sai mata masu juna biyu kawai ba.Daman ba iya mai juna biyu nankarwa ke fitowa ba?

6. Waɗanda suke da sabuban fitowar nankarwa sun haɗa da:

i. juna biyu: Kaso 8 cikin 10 na masu juna biyu nankarwa na fito musu.

ii. waɗanda suke cikin shekarun balaga.

iii. Wanda ya rame ko ya yi ƙiba nan da nan.

7. Ga masu juna biyu, nankarwa na bajewa ko ta tsutstsuke bayan haihuwa.

8. Wasu nau’in mayukan shafawa suna iƙirarin magance nankarwa, sai dai babu ƙwararan dalilai da suka tabbatar da iƙirarin nasu.

9. A likitance, nankarwa, musamman ga masu juna biyu, ba ta da wata matsala. Sai dai idan akwai ƙaiƙayi ko kuma damuwa game da munin da nankarwar ke haifarwa ga fata, za a iya tuntuɓar likitan fata.

10. Har wa yau, a tuntuɓi likita idan nankarwa ta yi faɗi sosai tare da bayyanar tarun kitse / teɓa a ciki, wuya da ƙirji domin hakan na iya zama alamun wata cutar daban.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button