Labarai

DA ƊUMI-ƊUMI: Sarauniya Elizabeth ta mutu tana da shekara 96

Sarauniya Elizabeth ta biyu, wacce ita ce mafi daɗewa a tarihin ƙasar Burtaniya, ta mutu.

Elizabeth ta mutu tana da shekaru 96 a duniya.

“Sarauniyar ta mutu cikin lumana a fadarta da yammacin yau,” in ji fadar Buckingham, a cikin wata sanarwa da yammacin yai Alhamis. “Sarki da Sarauniya Consort za su kasance a Balmoral a yammacin yau kuma za su koma London gobe.”

Mijin Sarauniyar, Yarima Philip, ya riga ta rasuwa, wanda ya rasu a ranar 9 ga Afrilu, 2021, yana da shekaru 99 a duniya.DA ƊUMI-ƊUMI: Sarauniya Elizabeth ta mutu tana da shekara 96

Sarauniya Elizabeth ta bar ‘ya’yanta maza uku, Yarima Charles, Andrew da Edward; da kuma mace, Gimbiya Anne; jikoki takwas, Yarima William da Harry na Wales, Gimbiya Beatrice da Eugenie na York, da Peter da Zara Phillips, da kuma Lady Louise Windsor da James, Viscount Severn. Ta kuma rasu ta bar jikoki 12.

Wani labari : Kwamitin Zartaswa na PDP ya jaddada goyon bayansa ga shugabancin Ayu

 

Kwamitin zartaswa na jam’iyyar PDP na Ƙasa, NEC, ya kada kuri’ar amincewa da kwamitin gudanarwa na jam’iyyar na kasa (NWC).

Ndudi Elumelu, shugaban marasa rinjaye na majalisar wakilai ne ya gabatar da kudirin a taron hukumar zabe a ranar Alhamis.

Mukaddashin shugaban kwamitin amintattu na jam’iyyar (BoT) Adolphus Wabara ne ya gabatar da kudurin wanda dan jam’iyyar Ishola Balogun Fulani daga jihar Kwara ya amince da shi.

Hakan na nuni da cewa shugaban jam’iyar PDP na ƙasa, Iyochia Ayu ya tsallake rijiya da baya.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button