Labarai

Bidiyon Yadda Ɓarayin Daji Sukayi Yunƙurin Shiga Wani Gida A Funtua

Bidiyon Yadda Ɓarayin Daji Sukayi Yunƙurin Shiga Wani Gida A Funtua.
Bidiyon Yadda Ɓarayin Daji Sukayi Yunƙurin Shiga Wani Gida A Funtua

Lamarin ɓarayin daji yana ƙara ta’azzara a jihar Katsina kamar yadda zaku gani a cikin wannan bidiyo, daren ranar Juma’ar da ta gabata ne 02/09/2022 da misalin ƙarfe 10:20 na Dare masu garkuwa da mutane suka shiga gidan wani Electrical Engineer a garin Funtua jihar Katsina.

Allah cikin Ikonshi ya sa mutumin baya gida tare da iyalansa, masu gadin gidan kuma da suka lura da zuwan Ɓarayin sun gudu domin tsira da rayukan su, ƴan ta’adar sun samu nasaran karya kofar shiga Gidan ta farko wato gate suka shiga gidan, amma basu iya balle kofar shiga cikin falo da dakunan gidan ba.

Shi kuma Mai gidan ya kafa CCTV Camera suna Naɗar faifan bidiyo na duk abinda yake faruwa a gidansa ko da baya nan, da yake masani ne na Na’urori ya haɗa CCTV Camera ɗin da wayar shi ta salula.

Kasancewar Alla bai basu ikon shiga Gidan ba, hakan yasa suka fita daga gidan, suka shiga wata unguwa da ake kira Project Quarters Funtua suka ƙwashi mutane da yawa suka tafi dasu Daji, wannan yanayin dai shike ta faruwa a Ɗan tsakanin nan a ƙananan Hukumomin Bakori da Funtua.

Al’amarin nan dai abu ne mai Matuƙar tada hankali, ko a satin da ya gabata Ƴan Ta’adar Nan sun sakama wata Motar sulke ta Jami’an tsaro wani abun fashewa a ƙaramar hukumar Jibia Lamarin da yayi sanadiyyar rasa rayukan wasu Jami’an tsaro tare da jiggata wasu, amma ganin yadda Gwamnati ta sayo Motocin sulke domin tunkarar Lamarin hakan yana Ɗan sanyaya zukatan Al’umma.

WANI LABARI : labari mai dadi Akan Case Din Dcp Abba Kyari

 

Yau an gabatar da Sarkin Yakin Nigeria DCP Abba Kyari a Kotu kan batun bukatar hukumar FBI na mikashi Kasar Amurka domin ya amsa tuhuma akan alakarsa da dan damfarar yanar gizo Hushpuppi

Kotu ta yi watsi da batun bukatar mika DCP Abba Kyari Kasar Amurka dogaro da kundin tsarin Extradition Section 3 (6) (a), Section 6 of Extradition Act wanda Kotu bata samu DCP Abba Kyari da laifi ba

Daga yau Kotu ta rufe babin case din DCP Abba Kyari da hukumar FBI na Kasar Amurka saboda ba’a sameshi da laifin hada baki da madamfari Hushpuppi ba kamar yadda akayi zargi

‘Yan uwa ku tayamu murna, yau makiyan Sarkin Yaki da wakilan kidnappers da IPOB ba zasuyi bacci ba, ALHAMDULILLAH saura case din hukumar NDLEA

Jinjina ga babban Lauya abokina Barr. Hamza N Dantani wanda yayi tsayuwar daka har wannan nasara ta tabbata da ikon Allah

Yaa Allah Ka daukaka darajar DCP Abba Kyari, Ka kunyata makiyansa na fili da na boye

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button