Labarai

(Bidiyo)Karfin hali sata a gidan yan’ bindiga: Masu garkuwa sun kama barawo dake yi masu sace-sace a gidajensu

Advertisment

Wasu gungun yan bindiga a kauyen Kilili na jihar Katsina sun kama wani matashi da suka ce baraw0 ne dake zuwa gidajen su yana yi masu barna yana sace karafuna da sauran kayayyaki a gidajensu.

A wani bidiyo da Taskar Labarai  ta kalla an ga yadda yan bindgar suka daure matashin mai suna Halliru wanda ya ce shi dan kauyen Ranka ne, sannan suka gabatar dashi ga yan jarida kafin daga bisani suka mika shi ga hukumar soji domin a dauki mataki akansa.

Alh Usman Kachalla Rugga shine shugaban yan bndigar wanda ya shaidawa dan Jarida Usman Saleh Jino cewa dama sun dade suna neman kama masu zuwa suna yi masu sace-sace a gidajensu sai gashi yau Allah ya basu sa’a sun kama baraw0n,

Ya ce sunyi niyyar kashe shi to amma suka yanke shawarar gayyatar yan jarida cikin dajin domin nunawa Gwamnati irin kokarin da suke yi wajen kama ba tagari, “kuma yanzu zamu baku shi a kaishi wajen hukuma su hukunta shi”

Ga Bidiyon nan ku kalla.

WANI LABARI : Sakatariyar Harkokin Wajen Birtaniya, Mary Elizabeth Truss, ta zama sabuwar Firayim Ministar Birtaniya.

 

Truss, mai shekaru 47, ita ce mace ta uku da ta zama Firayiminista na Burtaniya bayan Iron Lady, Margaret Hilda Thatcher da kuma Theresa Mary May.

Taskar Labarai  ta ruwaito Truss ta doke tsohon Shugaban Exchequer, Rishi Sunak ta samu nasara kamar yadda Sir Graham Stuart Brady, Jami’in zaben ya sanar.

Rishi Sunak MP ya samu kuri’u – 60399

A yayinda Liz Truss MP ta samu – 81326

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisment
Back to top button