Bana Mining Pi Network Kamar Yadda Mutane Suke Yaɗawa – Naziru Sarkin Waka
A cikin yan kwanakin nan mutane a shafukan sada zumunta sun fitar da wasu bayyanai masu nuna cewa sarkin waka yana pi Network mining wanda abun ya kawo cece kukce to sai gashi ya fito ya wanke kansa da kansa na cewa shi sam bayayi kamar yadda shafin Amihad na ruwaito
Mun ci karo da wani rubutu a shafin Fesbuk wanda marubucin yace: “Zuwa yanzu mun gama hada duk wasu hujjoji da suka tabbatar da naziru sarkin waka shima yana cikin masu yin Mining na Pi network”
“Dama masu kudi wasu ance babu wanda ya kaisu kyashi da hassada kar wani yazo kusa dasu ballantana ma ya kamo su”
Ban ga hikimar da kana yin abu a boye sannan kazo media kana zagin masu yi ba.”
“Ita harkar crypto da mining da platform harka ce da baka isa kanayi ba wanda ya sani ba duk kukewa sai anzo inda za’a gane kana yi in ma kai baka bayyana ba.”
Sarkin Waka ta hanyar wani bidiyo daya wallafa a shafukansa na sada zumunta wanda yake cewa an kirashi a waya ance anga nombarsa yana mining Pi.
Ta haka ne yace shi baya mining Pi be ma san ya pi yake ba ya dai san ma’anar mining amma wani abu daya danganci Pi bai san ko yadda app dinsu yake ba.
Ya kara da cewa shi yanzu abubuwa guda biyu ne wanda yake ya ga anyisu an gama lafiya a kasar nan.
Na farko yace bashi da burin daya wuce ya anyi zabe me gabatowa lafiya kuma an gama lafiya.
Na biyu kuma shine fashewar Pi ko fashewar yan Pi, inda yace dole a samu daya daga ciki.
Ka zalika sauraran maganganun da yayi zaku iya saurararsu cikin bidiyon dake kasa.
Kamar yadda kuka sani Sarkin Waka yayi wannan jawabine biyo bayan yadda mutane suke wallafa abubuwan da suka shafe a shafukan sada zumunta inda suke cewa shima yana mining Pi.