Labarai

Ango ya kama babban Amininsa tare da Matarsa A Hotel sati Daya Da Aurensu

Majiyarmu ta samu wani labari mai ban takaici tare da ban mamaki irin yadda wannan matar da abokinsa sunka cucesa kamar yadda shafin amihad na ruwaito.

Mun samu labarin wani Ango Ya Kama Matarsa ​​A Otel Tare Da Babban Abokinsa Mako Ɗaya Da Auren.

Wani Ango ɗan Najeriya da ya yi aure ya kama matarsa tana tsaka da lalata da abokinsa Otal.

An ga wani faifan bidiyo da ya ɗauki hankulan mutane inda ya yaɗa matarsa da abokinsa a wani otel yayin da suke tsaka da holewar su.

Rahotanni sun bayyana cewa ma’auratan sun yi aure kwanan nan, don haka abun ya matuƙar ɓata masa rai sosai inji shi angon.

Ango ya ce tun da farko ya gargaɗi abokin nasa mai suna Dennis da ya guji matarsa bayan ya ga suna wata mu’amala wacce bai gane mata ba.

Amma sai bai ji ba, ya ci gaba ba har sai da na kama su da hannuna a wani ɗakin Otal inji shi.

A cikin faifan bidiyon, ana iya ganin shi yana caccakar abokin nasa wanda ya tarar da matarsa har ta ɓoye a banɗaki, inda Ango ya ke tambayar matar ta dalilin da ya sa ta ci masa amana.

[Via]

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button