Ango Ya Fasa Auren Amarya Bayan Ta Ƙi Sanar Da Shi Wanda Ya Siya Mata iPhone 13 Pro Max
Wannan angon yana da gaskiya saboda cewa Gaskia babu wanda zai yarda yaga budurwarsa da zai aure da iPhone 13pro max kamar yadda shafin Dokin karfe Tv na ruwaito.
Wani ango ya fasa auren amarya ana gab da aurensu, bayan ya ga budurwar ta sa da sabuwar waya ƙirar iPhone 13 Pro Max wacce yanzu haka ta kai naira dubu ɗari takwas da talatin (N830,000).
Wannan ya sa ya zauna da ita don jin inda ta samu wayar. Sai dai duk yadda yayi da ita ta ƙi yarda ta sanar masa, wannan lamarin ya hassala shi ya fasa aurenta.
WANI LABARI : An sace makarar daukar gawa a wani masallaci a Kaduna
Wani dan Jarida Shuaibu Abdullahi ya bayar da labarin cewa makarar da aka sace ta karfe ce a wani masallaci dake Unguwar Hayin Banki, har ma ana danganta batun da masu siyar da karfe a kan sikeli a cikin Unguwanni wato yan gwan-gwan.
Yace Limamin Masallacin ne ya fada a yayin hudubar Juma’a, inda yayi tsokaci tare da jan hankali kan satar kayan mutane musamman a masallatan Unguwanni.