Labarai

An Kame Wani Malami Da Laifin Yin Fyade Da Karamar Yarinya

Jami’an ‘yan sanda sun kama wani Fasto mai suna Michael Abiodun dan shekara 48 da haihuwa a cocin The Light House Gospel Oluwo, Owode Egba a karamar hukumar Obafemi Owode a jihar Ogun, bisa zarginsa da yin lalata da wata matashiya ‘yar shekara 12 da haihuwa a cocinsa shafin Rigar Yanci International na ruwaito.

An gano cewa mahaifiyar wadda abin ya shafa ta shiga cocin ne sakamakon matsalolin da ta tsinci kanta na tsafi a ciki, wanda ta yi ikirarin cewa ya kai ga mutuwar ‘ya’yanta mata biyu.

Ta shiga cocin don neman ceto da kuma kawar da ƙarin asarar yara.

An ci gaba da cewa Fasto, mai ‘ya’ya uku, ya bukaci mahaifiyar wanda iftila’in ya afkawa da ta aiko masa da ‘yarta domin yin addu’a ta musamman amma ya shigar da yarinyar cikin daki a cikin cocin ya yi mata fyade wanda hakan ya kai ga ta samu ciki.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan, Abimbola Oyeyemi, ya shaida wa manema labarai cewa, jami’in ‘yan sanda reshen Owode Egba, Olasunkanmi Popoola, ya yi karin bayani kan jami’an da suka gudanar da bincike a wurin, tare da kama Fasto.

SP Oyeyemi ya ce faston ya amsa aikata laifin yayin da ake yi masa tambayoyi amma ya dora laifin a kan sharrin shaidan.

Ya kuma amince cewa shi ne wanda ya lalata yarinyar, dalibar karamar sakandare ta aji 2, a cewar kakakin ‘yan sandan.

Mahaifiyar wanda lamarin ya shafa ta bayyana wa ‘yan sanda cewa tun da ‘yarta ta daina yin haila a baya, da wuya ta san tana da ciki sai bayan wata bakwai.

“Matar wadda ta haihu watanni uku da suka gabata ta sanar da ‘yan sanda cewa Fasto ya yi mata barazana kan mummunan sakamako idan ta sanar da kowa abin da ya faru a tsakaninsu, kuma shi ya sa ba ta sanar da mahaifiyarta ba. ” in ji Oyeyemi.

Za a mika wanda ake zargin zuwa sashin binciken manyan laifuka na jihar domin ci gaba da bincike da gurfanar da shi gaban kuliya.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button