Labarai

An bukaci DSS ta kamo Gumi ta bincike shi – Ko a barke da zanga-zanga

Bayan kama Tukur Mamu wanda jami’an Dss sunkayi a satin da ya gabata wanda har an gurfanar da shi a gaban kotu wanda kotu ta bayar da umurnin hukumar Dss taci gaba da tsare shi har da nan zuwa kwana 60 wanda majiyarmu ta samu wani labari daga shafin taskar labarai cewa wata kungiya tana barazanar cewa ya zama dole a kama shi domin shima yana zaman sulhu da yan bindiga.An bukaci DSS ta kamo Sheikh Gummii ta bincike shi – Ko a barke da zanga-zanga

Wata kungiyar farar hula, mai suna Coalition for Peace In Nigeria (COPIN), ta yi kira ga hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) da ta gaggauta kama fitacen malamin addinin musuluncin nan mazaunin Kaduna, Sheikh Ahmad Abubakar Gumi, ta tuhume shi bisa zargin da ake masa na hulda da ‘yan bindiga/’yan ta’adda.

A cewar COPIN, ya kamata a gayyaci Gumi ya amsa tambayoyi duba da yadda ya rika shiga dazuka ya yi magana da ‘yan fashi da masu garkuwa da mutane da ke barazana ga tsaron kasa, sannan da yadda kuma ya ci gaba da kira ga gwamnatin tarayya da ta yi wa ‘yan ta’addan afuwa.

A cikin wata sanarwar hadin gwiwa mai dauke da sa hannun shugaban kungiyar na kasa Pharmacist Emeka Akwuobi da Hajiya Fatih Yakub Sakatariyar kungiyar ta kasa, kungiyar masu fafutukar neman zaman lafiya ta ce Gumi na da bayanai da dama da zai bayar kan ayyukan ‘yan bindiga, musamman wadanda ke aiki a yankin Arewa maso Yamma.

“Kungiyar ta dage da cewa ta gaggauta kama malamin tare da gurfanar da malamin a gaban kuliya musamman ganin yadda aka kama Tukur Mamu wanda shine ke magana da yawun Dr Gumi.

Kungiyar ta kuma kara da cewa kama Gumi yana da matukar muhimmanci wajen gudanar da zabe cikin kwanciyar hankali, la’akari da yadda zai baiwa hukumar leken asiri wasu muhimman bayanai masu inganci a kan hakikanin wuraren da ‘yan ta’addan ke aiki, da kuma yadda har zai kai ga a iya kama su.

Kungiyar ta yi barazanar shirya zanga-zangar lumana a Abuja, da sauran garuruwa, idan hukumar leken asirin ta kasa gayyatar Gumi.”

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button