Amarya Ta Ki Sumbatar Ango A Lokacin Bikin Aurensu Saboda Angon Yana Warin Baki
A wani rahoton da hausaloaded na samu wanda wani marubuci ya wallafa a shafinsa mai suna Aliyu Adamu Tsiga ya ruwaito wani labari mai ban mamaki wanda akwai ban dariya da a’ajabi, ga yadda rahoton ya bayyana.
“A haƙiƙa, sun nuna jin daɗinsu ga kowa da kowa don yaɗa faifan bidiyon da aka yi niyyar yi musu izgili. Bidiyon farko ya ba da labarin wata amarya da ta ki sumbatar angonta saboda zargin bakinsa yana wari. Mutumin ya yi iya ƙoƙarin sa, amma matar ba ta bar shi ya dasa mata laɓɓansa ba. To, daga baya ya fito cewa, macen ta kasance mai kunya wadda ba ta san yadda za ta yi ta sumbance ni ba a idon jama’a.
Ko dai a kan warin ango ne ko kuma tawali’u na amarya, ma’auratan sun fito suna nuna farin cikin su da yadda suka zama abin zance a cikin gari a daidai wannan lokacin. Sun ce cikin murmushi a cikin wani faifan bidiyo, “Muna gode wa ƴan Ghana saboda aikin da kuka yi mana. Kun sanya mu shahara sosai don haka muna godiya gare ku.”
Karanta wani labari: Amurka na Neman dan Nijeriyan da ya damfareta dala Miliyan talatin (30)
Hukuman binciken manyan laifuka ta amurka FBI na farautan wani dan asalin kabilan igbo a nijeriya bayan ya damfari gwamnatin New york kudaden da yawansu ya zarta dala miliyan talatin, kwatankwacin naira biliyan 15.
Wata sanarwa da ofishin babban lauyan amurka ta fitar tace, ana tuhuman Chidozie Collins Obasi mai shekaru 29 kan aikata laifuka da dama da suka hada da damfara ta hanyan amfani da sakonni ta yanan gizo
A farko-farkon barkewan Covid 19, obasi yayi ta sayarma asibitoci da cibiyoyin kiwon lafiya na amurka na’uran numfashi na bogi, kafin daga bisani ya saci bayanan wani ba amurke, inda yayi ta karban kudaden rage radadin covid 19 da sunan shi
Hukumomin amurka sunce, obasi bashi kadai bane yake aikin damfaran domin kuwa yanada wasu mataimaka a kasan Kanada, amma daga nijeriya yake gudanar da nashi aiyuka na damfara
Muddin dai FBI tayi nasaran cafke shi, obasi na iya fuskantan zaman gidan yari na tsawon shekaru 621 da kuma cin shi taran dala miliyan 5 da dubu 750
Haka zalika hukumomin na amurka zasu tilasta masa dawo da dukkanin kudaden da ya sace da suka zarta dala miliyan 31.