ALBUM: Sanarwa Akan Sabon Album ALKALI – Abdul D One
kamar yadda anka saba a duk shekara fitaccen mawakin nan Abdul D One yana fitar da album kuma yana gamsar da masoyansa da nishadantarwa a cikin wakokinsa to ko wannan shekara fitaccen mawakin yayi kokari wajen kawo muku sabon kudin album dinsa wanda yayiwa take da suna “ALKALI”
Abdul D One ya fitar da wannan sanarwa a shsfinsa na sada zumunta inda yake gayawa masoyansa cewa tabbas wannan shekarar ma ba’a barshi a baya ba yana nan zuwa.
“Assalamu alaikum warahamatullah masoyana masu bibiyar abubuwa kamar yadda kunka sani suna na Abdul D One nasan kunji shiru kwana biyu wasu na tambaya ko amarya ta boye ni
Ko na daina waka ne ban sani wakoki ba duk da dai ana sakin wasu ba kamar yadda anka saba ba na kan saki album duk shekara wanda ko wannan shekara nazo kuma da ALKALI album wanda in sha Allah za’a sake shi a Ranar 06/09/2022 a ranar talata kenan in sha Allah.
Zamu saki ALKALI album a kowane platform duk wanda kuke samun wakokin kamar apple music YouTube,audiomack duk dai wani platform da ake sakin wakoki boomplay da dai sauransu.
Saboda haka kada ku bari a baku labari na nesa da kusa da wanda baida waya zai iya nemansa wajen yan downloading alkali album yana tare da ku in sha Allahu.”
https://www.instagram.com/reel/Ch79EFrgVd8/?igshid=YmMyMTA2M2Y=
Idan baku manta a shekarar da ta gabata mawakin ya nishadantarku da album mai suna NABEELA wanda tabbas masoyansa sunyi na’am da wadannan wakoki domin sun nishadar da su.