Fitaccen malamin addinin Musulunci nan, Shaikh Habibu Yahaya Kaura, ya ce sadaki shi ne ruhin aure, amma a yanzu zamani ya zo ba a daukarsa da muhimmanci.
Malamn ya ce a wannan zamani ana kashe makudan kudi wajen al’adun aure amma idan an zo kan sadaki sai a a tsuke bakin aljihu.
Sheikh Habibu Yahaya Kaura ya bayyana haka ne a wajen taron daurin auren ’ya’yan Babban Limamin Masallacin 1004, Sheikh Ibrahim Sulaiman, wanda aka yi a ranar Lahadin da ta gabata a cikin garin Legas kamar yadda majiyarmu hausaloaded ta samu tattara bayanai daga shafin Amihad.
Ya ce za ka ga idan auren mawadaci ne zai iya kashe Naira miliyan goma a al’adun da aka jingina wa aure, amma idan an zo kan sadaki sai ka ga an bayar da Naira dubu 50, alhali sadaki Musulunci ya shirya shi domin amarya ta samu abin da za ta yi hidima.
Ya ce shi sadaki ba na iyaye ba ne, hakkin amarya ce, yanzu sadaki akasari ko katifa ba ya saye.
Sheikh Habibu Kaura ya ce wasu na dogara ne da Hadisin da ke nuna cewa aure mafi albarka shi ne wanda sadakinsa ya zama kadan, inda ya ce amma kadan din ne ba a san ma’auninsa ba.
“Babu wanda sadakin da ya gaza Naira miliyan hudu a kudinmu na yanzu a auren ’ya’yan Annabi (SAW), domin babu sadakin da ya kasa Dirhami dari biyar wanda ya kai daidai da Naira miliyan hudu na Najeriya.
Saboda haka mayar da sadaki Naira dubu hamsin tozartar da aure ne, alhali mutum na jira in an kai masa amarya a kai masa abincin da zai ci na shekara guda da gadonsa da komai har cokalin da zai ci abinci duk sai an kai masa,” inji shi.
Ya ce, “Don haka sai a duba kowane bangare abin da al’ada ce ta takura wa aure sai a rage amma bangaren al’amarin shari’a sai a habaka shi, domin sadaki ba ya da iyaka.
Malikiyya ne suka ce kada ya yi kasa da rubu’in Dinari, shi ko rubu’in Dinari yanzu bai kai Naira dubu talatin ba, kada ya yi kasa suka ce, amma sama ba ya da iyaka.”
Shehin Malamin ya ce “Wasu malamai ma sun ce kasan ma ba ya da iyaka, kuma gwargwadon darajar mace gwargwadon sadakinta.
“Ba za ka dauko yarinyar da iyayenta suka yi mata tarbiyya ta haddace Alkur’ani Mai girma ko ta yi makarantar ta har ta yi digiri, ko ta iya abinci ta iya komai tana da tsari ka hada ta da wadda ba ta san komai ba, ka ce duk dubu hamsin sadakinsu wannan ba daidai ba ne.”
Tun farko ana gabatar da waliyyan angwayen uku dab da daurin auren, inda kowanensu ya gabatar da sadakin Naira dubu 50, nan take Sheikh Habibu Yahaya Kaura, ya ja hankulansu, ya nuna cewa sadakin dubu hamsin-hamsin