AddiniLabarai

Ƴar shekara 13 ta haddace da rubuta Alkur’ani a Katsina

Allah Akbar tabbas wannan labari yayiwa dukkan Musulmi dadi duba da irin wannan baiwa da Allah ya baiwa wannan hafiza Allah ya sanyawa karatun ta albarka amin mun samu Wannan labari daga Jaridar Daily Nigerian Hausa na ruwaito.

Ƴar shekara 13 ta haddace da rubuta Alkur’ani a Katsina
Ƴar shekara 13 ta haddace da rubuta Alkur’ani a Katsina

Wata yarinya ‘yar shekara 13, mai suna Zuwaira Ahmed da ke ƙauyen Kagara a Ƙaramar Hukumar Kafur ta jihar Katsina, ta haddace tare da rubuta cikakken Alkur’ani izu 60.

Da ya ke jawabi a wajen bikin karrama yarinyar a yau Asabar, Hakimin Mahuta, Bello Abdulkadir, ya bayyana farin cikinsa da wannan ci gaba.

Ya bayyana cewa wannan babbar nasara ce ga al’umma, da ma jihar baki ɗaya, musamman a ɓangaren ilimin addinin Musulunci.

Abdulkadir ya kuma yabawa iyaye, malamai da sauran shugabannin al’umma kan yadda su ke kula da tarbiyyar ƴaƴansu yadda ya kamata, yana mai kira gare su da su ci gaba da yin hakan.

Danejin Katsina, ya baiwa sarakunan jihar tabbacin cigaba da bada goyon baya ga duk wani abu da ya shafi addinin musulunci, domin cigaban yankin baki ɗaya.

Shugaban karamar hukumar Kafur, Garba Kanya, ya yaba da kwazon yarinyar tare da bada tabbacin tallafa mata a matakin sakandire da manyan makarantu.

Shugaban makarantar ta, Madrasatul Tahfiz, Sheikh Sani Kagara, ya ce an kafa makarantar ne da nufin yin tasiri na ingantaccen ilimin addinin Musulunci a tsakanin matasa a cikin al’umma.

A cewarsa, yarinyar ta haddace Alkur’ani ne a cikin shekaru huɗu, kuma ya danganta nasarar da ta samu ga goyon bayan iyayenta da jajircewar malamanta a makaranta.

A nasa jawabin, mahaifin hafizar, Ahmed Sani, ya yaba da duk tallafin da aka ba shi da ƴarsa, inda ya yi kira ga iyaye da su bar ƴaƴansu su samu ilimin addinin musulunci da na boko.

Ya kuma ba da tabbacin ci gaba da ba ta goyon bayan da ya dace don kuma ta ci gaba da karatun ta na yamma, inda ya ce a halin yanzu tana makarantar firamare a yankin.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button