Labarai

Yadda Wani Magidanci Ya Lakaɗawa Matarsa duka har lahira saboda Koko

Advertisment

Majiyoyi daga kauyen Kadaura na Karamar Hukumar Rafi a Jihar sun ce matar ta bakunci lahira ne bayan mijin nata mai shekara 20 ya lakada mata duka, ta yanke jiki ta fadi magashiyyan nan take rai ya yi halinsa.

Kakakin ’yan sanda a Jihar Neja, DSP Wasiu Abiodun, ya ce, “Wanda ake zargin ya amsa cewa ya yi matar tasa duka saboda dan sabanin da suka samu a kan koko.

“Nan take ta fadi magashiyyan, aka dauke ta ranga-ranga zuwa Babban AsibitinAsibitin da ke garin Wushishi inda likitoci suka tabbatar cewa rai ya yi halinsa.”

Kakakin ’yan sandan ya kuma tabbatar wa Aminiya cewa ’yan sanda na tsare da matashin magidancin a Babban Ofishinsu da ke garin Kagara, suna masa tambayoyi.

“An riga an fara bincike kuma da zarar an kammala za a gurfanar da wanda ake zargin a gaban kotu,” inji DSP Wasiu Abiodun.

Labarin kisan na zuwa ne mako guda bayan wani makamancinsa inda ake zargin wata matar aure da lakada wa kishiyarta duka da muciya har ta mutu, sannan ta kona gawarta.

Advertisment








Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button