Labarai

Yadda Matashi Ɗan Aikin Gida ya ɗirkawa ɗiyar mai gidansa ciki, ya zubar da cikin Sa’a nan ya sheƙata lahira tare da ƙone gawarta

Wani sarauyi mai shekaru 27 da haihuwa ya kashe budurwarsa mai Shekaru 13 har lahira.
Safiya Danladi ta gamu da ajalinfa ne bayan da Saurayinta Munkaila Ado ya kaita Gombe daga Bauchi domin a zubar mata da cikin daya dirka mata wanda ya kai watanni 6.

Matashi mai Aikin Gida ya ɗirkawa ɗiyar mai gidansa ciki, ya zubar da cikin Sa'a nan ya sheƙata lahira tare da ƙone gawarta
Ɗan Aikin da ya kashe yarinyar mai Gidansa

A lokacinda yake zantawa da manema labarai bayan da suka yi ram da shi. Ado yace uwar budurwar tasa tana sane da tafiya da yarinyar da yayi domin ya zubar mata ciki. Sai dai yace mahaifin yarinyar bai da labarin abunda ake ciki.

“Da mahaifiyar yarinyar muka hada baki domin na kaita a zubar mata da ciki. Mahaifinta bai sani ba shi yasa yake cewa ta bata”. Cewar Munkaila.
Inda yaci gaba da cewa, ” Na kaita garin Gombe ne a Unguwar Jeka Fari gidan wata mai suna Amina Abubakar mai shekaru 50. A nan ne matar ta baiwa Safiya wasu magunguna ta sha na zubar da cikin.Matashi mai Aikin Gida ya ɗirkawa ɗiyar mai gidansa ciki, ya zubar da cikin Sa'a nan ya sheƙata lahira tare da ƙone gawarta

“Akan hanyar mu na zuwa kauyen Mai’ari dake Akko Local Government sai ta soma mutsu-mutsu na ciwon ciki. Daga karshe sai ta mutu”. Ta bakin saurayin marigayiyar.

Ya ce bayan ta mutu ne da taimakon wani abokinsa suka bin neta a wani lungu bayan da abokin nasa ya kona gawarta saboda  kar a ganeta.
Tuni da ‘yan sandar jihar ta Bauchi a bisa umurnin Kwamishinan ta sun cafeke duk mutanen da suke da hannu a wannan ta’asar domin fuskantar hukunci.Matashi mai Aikin Gida ya ɗirkawa ɗiyar mai gidansa ciki, ya zubar da cikin Sa'a nan ya sheƙata lahira tare da ƙone gawarta

Da fatan samari da ‘yan mata zasu ji tsoron Allah wajen yin zina bayan sunyi ciki kuma suce zasu zubar.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button