Yadda Kyawawan Ƴan Mata Suka Bayyana A Wajen Bikin Ashenda Na Ƙabilar Tigarawa Dake Ƙasar Habasha
Bikin Ashada da Tigarawa ke gudanarwa duk Shekara daga ranar 16 ga watan Agusta har zuwa ranar 26 na kowane watan Agustan Shekara a yankin Tigray dake Ƙasar Habasha(Ethiopia) ,a tsakannin ƙabilu Tigarawa da Eritawa. Shafin Dokin karfe Tv na ruwaito
Ashenda! Bikine na Mata Zallah da ake yi a kowace Shekara a watan Agusta a garin Tigray na ƙasar Habasha, don tabbatar da farin ciki ga Mata, ya kan zo da abubuwa na kawata Jiki, Kwalliya, kaɗe-kaɗe da raye-raye, tare da rawa don girmama Darajar Mace, inda yan matan da suka halarci bikin sukan Samu kyaututtukan da suka haɗa da Abinci, da abun Sha, tare da kuɗaɗe daga Al’ummar baki ɗaya.
Ko da yake a wajen Tigar@wa, bikin yana da Asali a addini ake tunawa da shi tun da jimawa iyaye da kakanni, domin girmamawa ga Maryama, Mahaifiyar Ann@bi Isah A.S, da wani Namiji bai taba Hawanta ba(Kusantarta), inda tun daga lokacin aka mayar da Bikin wani fili na girmama Y’anci ga jinsin Mata,tare da kin amincewa da cin Zarafi da take Hakkin mata.
Bikin na Ashenda, wanda aka fi Sani da “RANAR MATA” ya kasance abun Jira da marmari ga yan Matan Tigarawa, wadanda suka kai munzalin Shekarun Balaga, sukanyi Shiri na musamman don Jira da tarbar bikin “Ashenda” a manyan Watanni.
Kafin zuwan ranar bikin, gungun ƴan matan, sukanyi Shirin Hutu, tare da siyan Sababbin Sutturu, ziyartar guraren gyaran Gashi,Shirya Ganguna(Domin cashewa), tare da Samo Ciyayin da suke kira da Ciyayen “ASHENDA”, wanda zasu Daura a kirjiinsu a madadin Suttura a ranar Bikin.