Wata sabuwa : Maishadda yayimin Abunda duk kannywood babu wanda yayimin- Lawal Kumurci
Fitaccen jarumin nan wanda yake fitowa dan daba a cikin fina finan hausa Wata Shuaibu lawal kumurci yayi tsokaci game da sabon fim din da ake dauka mai dogon zango wanda kamfanin mai shadda Global ke shiryaawa mai suna “Dan Jarida”.
Shuaibu lawal kumurci yana mai cewa:
” Kun ganin nan na rantse da Allah ba’a taba biyana kudin da anka biyani a wannan series ba, a duk fina finan da nayi ba.
Wanda anka bani naira dubu dari biyu ₦200k wanda kuma series fim shine wanda ba’a biya sosai akansa sai dai alhamdulillahi.
Yace tabbas mai shadda shine mutum na farko da ya biya kudi masu yawa a kan fim a masana’antar kannywood.”
An dauki wannan guntun bidiyon ne a wajen daukar fim fin wanda shafin Labarun kannywood a Twitter sunka wallafa
Jarumi SHUAIBU KUMURCI ya bayyana albashin da MAISHADDA ya biyashi a fim din DAN JARIDA (SERIES)… Jarumin yace an biyashi 200k wanda shine highest payment daya taba samu a rayuwar sa ta film. Dama Producer Abubakar B. MAISHADDA ya samu wannan shaidar.
Directed by @hafizubello pic.twitter.com/B2Je9KwTJy
— Labaran Kannywood (@Hausafilmsnews) August 8, 2022