Labarai

Wata Mata Ta kashe Mijinta saura kwana bakwai 7 a daura Aure

A wayewar safiyar yau mun samu wani mumunan labari da babu dadin ji inda wata mata ta hallaka mijinta saboda tsananin kishi irin na mata na hauka da jahilci.

Datti assalafy ne ya ruwaito wannan labarin a shafinsa na sada zumunta inda al’amarin ya faru a jihar birnin kebbin da ke arewa maso yamma.

Wannan bawan Allah Lauya ne, sunansa Barr Attahiru Ibrahim Zagga daga jihar Kebbi, yana da mata amma sun rabu sakamakon bakin kishi na jahilci da ta tayar saboda yana shirin kara aure

Yau saura kwana 7 a daura masa aure da sabuwar amaryansa da zai aura a Maiduguri, to sai shekaran jiya matarsa da suka rabu ta nemo ‘yan ta’adda suka tafi gidansa suka rutsashi, suka dinga caccaka masa wuka har sai da hanjin cikinsa ya fito

Wata Mata  Ta kashe Mijinta  saura kwana bakwai 7 a daura Aure
Katin Gayyatar Daurin Aure

‘Yan ta’addan sun samu nasaran tserewa, amma ita matar an kamata kafin ta tsere, yanzu haka tana State CID na jihar Kebbi

Zaku ga gashi har da invitation card dinsa zai kara aure, tsohuwar matarsa ta kashe shi saboda laifinsa kawai zai kara aure bata so

Muna fatan Allah Ya jikan Barr Attahiru, Allah Ya tona asirin duk wanda yake da hannu a kashe shi”

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button