Labarai

Uwargida Ta Tura Kanwar Miji Cikin Tukunyar Tafasasshen Ruwan Zafi

Duniya mai abun yayi yau kuma mun samu muku wani labari da majiyar ta samu a shafin rariya inda anka ruwaito wani abun mamaki.

Jami’an hukumar yaki da safaran Bil-adama (NAPTIP) sun cafke wata mata mai shekaru 24 Basira Sagiru, bayan ta tura kanwar mijinta cikin tafasashen ruwan zafi.

Jami’in dake kula da harkokin yada labarai tare da hulda da jama’a na hukumar, Joslah Emelore, ya tabbatarwa manema labarai faruwan hakan a birnin Abuja.

A cewar shi Basira ta tura kanwar mijin wanda ke zama da su cikin tafasasshen ruwan zafin ne bayan gardama ta shiga tsakaninsu.

Wacce aka yi wa raunin, Hasiya Ibrahim, ta ji rauni sosai, domin ruwan zafin ya kona mata ko’ina a jikinta kafin mutane su zo su cece ta a hannun matar dan uwan nata. Inda aka yi gaggawar garzayawa zuwa hedikwatar mu da ke Abuja.

Emerole ya ce wacce aka kona a halin yanzu tana hannun hukuma NAPTAP ana mata magani.

Ya kara da cewa bayan hukumar ta cafke wacce ake zargi, a nan take an fara gudanar da bincike akan lamarin, inda ya ce hukumar za ta san matakin da za ta dauka game da lamarin da zarar ta ida gudanar da bincikenta.

Wannan na daya daga cikin manufofin hukumar na hana kaskanta dan Adam ta hanyar aiki tare da jami’an tsaro don daukaka su, musamman mata da yara.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button